✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Isuhu Yellow a Zamfara

An kashe Isuhu Yellow a yayin wani rikicin da ya kaure tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga.

Ɗaya daga cikin ƙasurguman ’yan ta’addan da suka addabi al’umma a Jihar Zamfara da kewaye, Kachalla Isuhu Yellow ya kwanta dama.

BBC ya ruwaito cewa an kashe ƙasurgumin ɗan bindigar ne a yayin wani rikicin cikin gida da ya kaure tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga.

Bayanai sun ce lamarin ya faru da yammacin yau Alhamis, bayan ya ɗauki tsawon lokaci yana wasan ɓuya da jami’an tsaro da wasu daga cikin takwarorinsa shugabannin ƙungiyoyin ’yan bindiga.

Ɗan jarida mai bincike kan harkokin ’yan bindiga, Munir Fura-Girke ne ya tabbatar da kashe ɗan bindigar.

Isuhu Yellow ya yi fice ne wajen harkokinsa a yankunan Tsafe da Ɗansadau da ke jihar Zamfara.

Harin dakaru ne ya yi ajalinsa — Makama

Sai dai ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya, Zagazola Makama, ya ce Isuhu Yellow ya yi gamo da ƙarshensa a wani hari da dakarun rundunar Fansar Yamma suka kai.

A cewar Makama, Kachalla ɗan Isuhu ya shafe shekaru da dama yana razana al’umma a faɗin Zamfara, Katsina, da wasu sassan Jihar Kaduna.

Makama ya ce ɗan bindigar wanda ya sha jinin jama’a ya jagoranci munanan hare-hare, ya yi wa jami’an tsaro kwanton ɓauna, sannan kuma ya jagoranci garkuwa da mutane da sace-sacen shanu.

Isuhu ƙasurgumin ɗan bindiga ne da ya zama abun kwatance a Arewa maso Yammacin ƙasar, wanda ya yi ƙaurin suna wajen safarar makamai da karɓar kuɗin fansar waɗanda ya yi garkuwa da su.

Ɗaruruwan mayaƙansa sun addabi ƙauyuka wajen karɓa haraji tare da kashe duk wanda ya bijere musu.

Haka kuma, Ɗan Isuhu ya taka rawa wajen garkuwa da mutanen da aka sace a harin jirgin ƙasan nan na Kaduna, inda ya karɓi kusan naira miliyan 800 a matsayin kuɗin fansa.

Ta’addancin Isuhu Yellow ya ƙazanta a wannan wata na Ramadana, inda kusan kullum yana kashe mutum ɗaya a matsayin wani aiki na wajabci da ya riƙa

A makonnin bayan nan, Isuhu Yellow ya jagoranci hare-haren da ya sanya shi a sahun farko na mutanen da jami’an tsaro ke nema ruwa a jallo.

Daga cikin hare-harensa na bayan nan akwai wanda aka kai A Karamar Hukumar Tsafe wanda ya janyo mutuwar wani babban jami’an tsaro da ’yan bijilanti.

Wannan ƙari na kan hare-haren da ya saba jagoranta kusan kullum a kan hanyar Tsafe zuwa Yankara, inda suka tare matafiya da ƙone gidajen mazauna ƙauyuka makwabta.

Isuhu yana da kyakkyawar alaƙa da Adoro Alero, wani ƙasurgumin ɗan bindiga da Gwamnatin Katsina ta sanya tukwicin Naira miliyan 5 ga duk wanda ya taimaka wajen kama shi.