Wasu ’yan bindiga a ranar Lahadin da ta gabata sun kai harin ɗaukar fansar kashe ƙasurgumin ɗan ta’addan nan, Kachalla Isuhu Yellow da aka fi sani da Ɗan Isuhu.
’Yan ta’addan sun kai harin ne ƙauyen Keta da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, domin ɗaukar fansar kashe jagoransu da jami’an tsaro suka yi makonni biyu da suka gabata.
- Kotu ta daure ango wata 6 saboda likin kudi a bikinsa
- Gaza: Isra’ila ta kashe Falasdinawa 58 a awa 58
Mazauna sun ce maharan sun kashe mutum ɗaya yayin da suka ƙone motoci 11 sannan kuma suka wawushe kayayyaki a kantinan ’yan kasuwa a yayin harin.
Bayanai sun ce ana zargin ’yan ta’addan da suka kai wannan hari mayaƙan Adamu Aliero ne — yayan marigayi Ɗan Isuhu.
Kachalla Yellow wanda ake alaƙantawa da kai munanan hare-hare a Zamfara da kuma babbar hanyar Funtua zuwa Gusau, ya gamu da ƙarshensa ne a yayin wani artabu da wata rundunar haɗin gwiwa ta Asakarawan Zamfara da kuma jami’an ’yan sanda a ƙauyen Keta.
A yayin da wasu rahotanni ke cewa, Ɗan Isuhu ya yi gamo da ƙarshensa ne a hannun wasu ’yan ta’adda masu adawa da shi da ke yi wa Dogo Gide mubaya’a, wasu kuma na cewa dakarun soji ne suka kawar da shi daga doron ƙasa.
Wani mazauni Danjigba — wani yanki da ke makwabtaka da Keta — ya tabbatar da cewa an kashe Isuhu Yellow ne a yayin da yake yunƙurin yi wa jami’an tsaro kwanton ɓauna a hanyarsu ta zuwa ƙauyen Keta domin kai ɗauki.
“Shi da mayaƙansa sun yi ƙoƙarin yi wa jami’an tsaron kwanton ɓauna amma a yayin musayar wuta da su aka kashe shi tare da mayaƙansa da dama.”
Ya ƙara da cewa, ragowar ’yan ta’adda a hanyarsu ta tserewa sun kai wa mazauna Danjigba hari, inda suka kashe mutum takwas ciki har da wani ɗan uwansa da wawushe kuɗi a hannun ’yan kasuwa.
Duk da aukuwar wannan hari, sai dai mazauna suka yi murnar mutuwar Isuhu Yellow, suna masu bayyana shi a matsayin marar imani wanda ya ɗauki alhakin sacewa da zubar da jinin mutane da dama a Tsafe, Gusau, Dan Sadau da kuma Funtua.
Kakakin rundunar ’yan sandan Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da kashe Isuhu Yellow a wani aikin haɗin gwiwa na jami’an tsaro da suka daƙile harin da aka kai ƙauyen Keta.