✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara

Mutuwar Ɗan Mudale ne zuwa bayan sa’o’i da kashe Kachalla Isuhu Yellow, wani ƙasurgumin ɗan bindiga da shi ma ya addabi Zamfara.

Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Ɗan Mudale da ya addabi mazauna yankin Tsafe da kewaye.

Rundunar ta ce a jiya Alhamis ne ta daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙauyen Keta da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta jihar.

Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar ya fitar a Gusau, babban birnin jihar.

A cewar DSP Yazid, a yayin daƙile harin ne ’yan sanda suka kashe gomman ’yan bindigar ciki har da Ɗan Mudale wanda ya addabi al’ummar yankin.

Ya ce rundunar haɗin gwiwa da ta haɗa da ’yan sanda da askarawa da kuma mafarauta ce ta yi karon batta da ’yan ta’addar da aka riƙa musayar wuta.

Sai dai ya bayyana takaicin cewa wani jami’in ɗan sanda daya da askarawa huɗu da kuma mafarauta sun bayar da ransu a yayin artabun.

Sanarwar ta ce a halin yanzu wasu mafarauta biyu na karɓar magani a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Gusau.

Kazalika, rundunar ’yan sandan ta ƙara jaddada ƙudirinta na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Ta yi kira ga mazauna da su riƙa gaggauta miƙa mata rahoton duk wani motsi da su aminta da shi ba domin a ɗauki matakin da ya dace.

Mutuwar Ɗan Mudale ne zuwa bayan kashe Kachalla Isuhu Yellow, wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ke sahun waɗanda suka jagoranci kitsa harin da aka kai jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja shekaru biyu da suka gabata.