Kasurgumin dan ta’addar nan da ke addabar yankin Sakkwato ta Gabas da Zamfara, Kacalla Bello Turji ya kashe manoma 11 a garin Lugu cikin Karamar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato.
Dan gwagwarmaya da ke biye da lamarin rashin tsaro a yankin Sakkwato ta Gabas Bashiru Altine Guyawa ya sanar wa manema labarai cewa, Turji ya dawo daga yawon sallah ne ya far wa garin da hari.
- ’Yan bindiga sun kashe mutane 40 a sabon hari a Filato
- Boko Haram ta kashe mutum 300 ta kwace ƙananan hukumomi 3 a Borno — Ndume
“Turji da yaransa sun bar kauyensa na Fakai a Karamar Hukumar Shinkafi suka shiga wasu kauyukka a Karamar Hukumar Isa a hanyarsu ta komawa Fakai bayan sun gama yawon Sallah suka kashe manoma 11.”
Guyawa yana ganin laifin jami’an tsaro kan lamari, inda suka gaza daukar mataki kan bayanan sirri da suke da shi.
Dan majalisar dokokin jiha, Honarabul Aminu Boza ya ce, ya samu bayanin sai dai dan bindigar bai shiga yankin da yake wakilta ba a lokacin bikin Sallah.
Ya ce, “muna sane da cewa Turji ya shirya kai ziyara a gabashin Gatawa, a nan ne muka dauki mataki, mun je Sabon Birni, inda muka dauki matakin tsaro don kare faruwar hakan, shi ne dalilin huce haushinsa a kan manoma a Isa’’.
Akwai bayanan da ke nuna cewa, Turji ya tsaya a kauyen Tozai, ya kashe shugaban ‘yan sintiri na garin.
A lokacin da aka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i ya ce, jami’an soja ne kadai za su iya tabbatar da farmakin saboda su ne ke aiki a yankin.
Duk da sojoji sun ayyana suna neman Turji ruwa jallo, amma ya ci gaba da kai farmaki a kauyukkan gabashin Sakkwato.