✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Turji ya kusa komawa ga mahallici — Sojoji

ƙasurgumin ɗanbindiga, Kachalla Bello Turji wanda sojojin ƙasar suka daɗe suna nema ya kusa komawa ga mahalicci.

A ranar Alhamis ɗin nan ne rundunar sojin Nijeriya ta ce ana cigaba da farautar  ƙasurgumin ɗanbindiga, Kachalla Bello Turji wanda sojojin ƙasar suka daɗe suna nema sun ce ya kusa komawa ga mahalicci.

Rundunar ta bayyana cewa kuma kwanakinsa sun kusa ƙarewa.

Ta kuma yi watsi da iƙirarin da ake na cewa sojoji sun rage kai hare-hare kan makiyaya, ’yan bindiga, ɓarayin shanu da sauransu, inda ta ƙara da cewa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen kame Turji.

Wannan na zuwa ne kimanin kwana ɗaya bayan Turji ya kashe manoma 11 a garin Lugu da ke ƙaramar Isa ta Jihar Sokoto

An samu rahoton Turji yana dawowa ne daga ziyarar Sallah da ya kai wata unguwa a Isa, lokacin da ya kai harin.

Da yake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida a hedikwatar tsaro a yayin ganawa da manema labarai, daraktan watsa labaran na rundunar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Markus Kangye, ya ce za su iya ci gaba da farauta tare da ganin bayan manyan ’yan bindiga da ke cikin dazukan ƙasar nan.