Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da samun ɓullar cutar sanƙarau guda 300 a wasu ƙananan hukumomin jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Farouk Abubakar ne ya tabbatar da hakan a taron wayar da kan jama’a na kwana ɗaya da ƙungiyar raya unguwanni ta jiha (WDC) tare da haɗin gwiwar ma’aikatar lafiya ta jiha da hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar suka shirya a ranar Juma’a.
- Darasi daga rayuwar Dakta Idris AbdulAzeez Dutsen Tanshi
- ’Yan bindiga sun harbe mata 2 a gona a Kogi
Sai dai kwamishinan bai yi ƙarin bayani kan adadin mace-macen da aka samu tun watan Fabrairu da aka fara samun ɓullar cutar ba.
Ya ce har yanzu mutane 16 na ci gaba da karɓar magani a asibitoci yayin da sauran kuma aka sallame su.
A jawabansu daban daban, mai ba da shawara na musamman kan harkokin kiwon lafiya a matakin farko na jiha, Dakta Muhammad Bello Marnona, da babbar sakatariyar hukumar, Dakta Larai Aliyu Tambuwal, sun yaba da irin hangen nesa na shugabancin hukumar ta WDC.
Sun ce, ana iya rigakafin cutar kuma sun shawarci mutane da su ziyarci cibiyoyin lafiya da ke kusa don samun magungunan da suka dace a duk lokacin da suka fuskanci wata matsala.
Shima da yake tsokaci shugaban yankin Malam Ya’u Muhammad Danda wanda mataimakinsa Alhaji Faruk Umar Garba ya wakilta ya bayyana taron a matsayin wanda ya dace.
A nasa jawabin, Sarkin Musulmi Sultan Sa’ad Abubakar wanda Hakimin Gagi, Alhaji Sani Umar Jabbi ya wakilta, ya yaba wa Gwamna Ahmed Aliyu da jagororin gwamnatinsa na inganta lafiyar al’umma.