’Yan sanda sun damke shugaban wata kungiyar asiri bayan ya tafka mummunar ta’asa a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.
Dan ta’addan ya shiga hannu ne bayan ya kashe mutum hudu a wani coci a kauyen Azikoro da ke Yenagoa, a daren Laraba.
Rundunar ba ta bayanna sunansa ba amma kakakinta na jihar, SP Asinim Butswat cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, ya ce an kama wanda ake zargi ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Agustan 2020.
SP Butswat ya ce mutumin ya amsa laifinsa, yana kuma ba da hadin kai har ya kai su wata mafaka inda aka gano miyagun makamai ciki har da bindiga kirar AK-47 da alburusai.
A yayin ci gaba da bincike, jami’in ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Mike Okoli, ya tura karin jami’ai domin gano sauran ’yan kungiyar asirin da suka tsere.