Shugaban Burkina Faso, Roch Christian Kabore, ya kori Firaiministan kasar, Christophe Dabire, daga bakin aiki ranar Laraba, a daidai lokacin da zanga-zangar neman ya sauka daga mukaminsa ta dada tsananta.
Matakin na zuwa ne yayin da kalubalen tsaron da ya addabi kasar ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, musamman sakamakon hare-haren ISIS da Alqa’ida.
- Tirelar da jami’an Kwastam ke kokarin kamawa ta danne mutum 4 a Kwara
- Najeriya A Yau: Yadda Rusau Ke Jefa Rayuwar ’Yan Najeriya Cikin Kunci
Abubuwa sun dada tabarbarewa Shugaba Kabore ne a watan Nuwamba, bayan wani hari da ya yi sanadin kisan sojoji da ’yan sanda 49 da kuma fararen hula guda hudu, wanda ya kai ga zafafa kiran da ake masa kan ya yi sauye-sauye a kunshin gwamnatinsa.
Tuni dai shugaban ya yi wa Rundunar Sojin kasar garambawul.
Ofishin Shugaban Kasar dai ya karbi takardar ajiya aikin Firaiministan, inda ya a ranar Laraba ya amince da hakan.
A bisa dokokin Burkina Faso dai, ajiye aiki Firaiminista na bukatar dukkan ragowar jami’an gwamnati su ma su sauka daga mukamansu.
To sai dai tilas za a nada gwamnatin rikon kwarya har zuwa lokacin da za a kafa sabuwar gwamnati.
Dabire dai ya zama Firministan a shekarar 2019, sannan an sake nada shi a watan Janairun 2021, bayan an sake zaben Shugaba Kabore a wa’adi na biyu.