✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban karamar hukuma ya biya wa al’ummarsa kudin wutar lantarki a Katsina

Majalisar karamar Hukumar Jibia a Jihar Katsina ta hada al'ummar yankin da layi na musamman na Kamfanin Samar da Lantarki na Kasa (TCN)

Majalisar Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Kastina ta biya wa al’ummarta kudin wutar lantarki a kowane wata.

Shugaban Hukumar, Alhaji Bishir Sabi’u na cewa nan gaba za a kammala aikin layin da aka ware musu na musamman na Kamfanin Wutar Lantarki ta Kasa (TCN).

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito shi yana cewa karamar hukumar ta riga ta hada garin Jibia da layi na musamman na TCN domin garin ya rika samun wutar yadda ya kamata.

Ya ce, “duk da cewa an yi gwajin wutar, amma ba a riga an kammala aikin layin na TCN ba, kuma da ya fara aiki, al’ummar garin za su fara samun wutar lantarki tsawon awa 24.”

Honorabul Sabi’u wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Mohammed Lawal-Jibia, ya ce karamar hukumar ta kulla yarjejeniyar da Kamfanin Wutar Lantarki na Kano (KEDCO), domin biyan kudin wutar lantarki Naira miliyan biyu ga al’umma a duk wata.

Ya ce sun dauki matakin ne domin rage wa jama’a wahalar da suke fama da ita ta tsadar rayuwa, musamman lura da yadda matsalar tsaro ta addabi yankin.

Ya bayyana cewa mma duk da haka, masu sana’o’in da ke jan wutar lantarki sosai ba sa cikin masu cin gajiyar tagomashin.

Alhaji Mohammed Lawal-Jibia ya sanar da hakan ranar Alhamis a yayin karbar bakuncin shugabannin Kungiyar ’Yan Jarida ta Kasa (NUJ) a kai kai masa ziyarar aiki.

Shugaban Karamar Hukumar ya bayyana cewa an samu wannan nasara da makamancin sa aka samu a bangaren noma da ilimi da sauransu ne da sahalewar Gwamna Dikko Radda.

A cewarsa, matsalar tsaro a karamar hukumar ta ragu sosai, yana ai cewa gwamnan bai taba yin watsi da bukatar al’ummar Jibia kan sha’anin tsaro ba.

Hasalima, gwamnan ya ba da fili da za a gina gidaje 152 domin sake tsugunar da ’yan gudun hijira a karamar hukumar.

Jibia na daga cikin kananan hukumomin Jihar Katsina mafiya fama da hare-haren ’yan ta’adda, inda da wuya a yini ba tare da hari ba.