Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, Farfesa Mahmud Yakubu, ya mika ragamar shugabancin hukumar ga Air Vice Marshal Ahmed Mu’azu, a matsayin shugaban riko.
Mahmood Yakubu wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya sake ayyana sunansa a matsayin wanda zai sake nadawa shugaban hukumar a karo na biyu ya mika ragamar hukumar ce a ranar Litinin.
“Wa’adin mulkina da na takwarorina kwamishinoni biyar da aka nada mu tare ya kare a yau; kuma kuan sane cewa dole sai karin wa’adina da aka yi ya samu amincewar Majalisar Dattawa”, inji Mahmood, yayin mika ragamar hukumar ga shugaban na riko.
Ya ce bai dace ba ya ci gaba da rike mukaminsa fiye da ranar Litinin 9 ga Nuwamba, 2020 ba tare da amincewar Majalisa da kuma sake rantsar da shi ba.
Air Vice Marshal Ahmed Mu’azu, shi ne kwamishinan INEC mai wakiltar yankin Arewa maso Gabas da ke kula da jihohin Adamwa, Borno da Taraba.
Dan asali kuma haifaffen Gombe a ranar 6 ga Satumba, 1957, Air Vice Marshal Ahmed Mu’azu ya yi karatun firamare da sakandare a 1964 zuwa 1975 a tsakanin Gombe, Kaduna da kuma Maiduguri.
Ya shiga Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Soji (NDA) a 1976 inda aka yaye shi a matsayin hafsan sojin sama a 1979.
Ya ci gaba da aiki a rundunar hari har ya kai matsayin Air Vice Marshal a 2007 kafin ya yi ritaya don kashin kansa a 2013.