✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Ibo a Jihar Oyo ya yi na’am da haramta kungiyar IPOB

Jagoran kabilar Ibo a Jihar Oyo, Ezendigbo Dakta Aled Anozie ya yi maraba da matakin haramta kungiyar IPOB, mai fafutukar kafa kasar Biyafara da Gwamnonin…

Jagoran kabilar Ibo a Jihar Oyo, Ezendigbo Dakta Aled Anozie ya yi maraba da matakin haramta kungiyar IPOB, mai fafutukar kafa kasar Biyafara da Gwamnonin jihohin Kudu Maso Gabas suka dauka.

Ya ce, “matakin da gwamnonin jihohin Kudu Maso Gabas da hadin gwiwar dattawa da kungiyar Ezendigbo suka dauka na haramta kungiyar IPOB ya yi daidai, domin ba mu son komawa gidan jiya da aka yi yakin basasa da ya lakume rayukan miliyoyin mutane.”

Ya bayyana haka ne a yayin hira da Aminiya a Ibadan. Ya ce, “rashin adalci da irin yadda Gwamnatin Tarayya ta mayar da sashen Kudu maso gabacin kasar nan saniyar ware, ba tare da samar da masana’antu da kamfanoni domin samar da ayyukan yi ga dimbin matasan yankin ba, shi ne ya haifar da fafutukar da kungiyar ta IPOB take yi.”

Sai dai ya ce suna bayar da shawara ga dukkan masu wannan fafutuka da su bi hanyoyin lumana da yin taka-san-tsan ba tare da daukar doka a hannunsu ba. “Ina so ka sani cewa, babban abin da kabilun Ibo suka ki jini shi ne, rashin adalci da mayar da su saniyar ware a yankinsu amma kabilun Ibo masu son ci gaban kasar Najeriya ne kamar yadda ake ganinsu a sassa daban-daban na kasa suna gudanar da harkokin kasuwancinsu.

“Babu wanda yake goyon bayan irin wannan salo na fafutukar kafa kasar Biyafara da kungiya IPOB take yi,” inji shi.

Ya ce tura ce ta kai bango ga wadannan dubunan matasa da suke zaune babu aikin yi kuma suna kallo ana fifita sauran sassan kasa da abubuwan ci gaba, an kyale yankinsu ba a damawa da su, shi ne ya sa suke yin wannan fafutuka.

Da yake amsa wata tambaya, cewa ya yi ya kamata Gwamnatin Tarayya ta kirkiro karin jihohi 2 ko 3 a sashen Kudu maso gabas kuma ta samar da masana’antu a wannan sashe sannan kuma a lalubo hanyar da dan kabilar Ibo zai zama shugaban kasar Najeriya. Ya yi tambayar cewa, “me ne ne laifin kasancewar kabilar Ibo a matsayin shugaban kasar Najeriya? “Idan Allah Ya ba Shugaba Muhammadu Buhari koshin lafiya ya kammala zango na 2 na jagorancin kasa, to ya kamata a kyale kabilar Ibo ya zama shugaba a zaben shekara ta 2023.”

A kan batun sake fasalin Najeriya kuwa, cewa ya yi shi bai ga dalilin da ya sa wasu mutane suka kyamaci wannan tsari da yake ganin zai kawo wa Najeriya ci gaba fiye da halin da take ciki a yanzu ba.