✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Hukumar NSC ya samu lambar yabo kan shugabanci nagari a hukumomin gwamnati

An karrama Shugaban Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC) da lambar yabo bisa kan shugabanci nagari wajen tafiyar da ma’aikatun gwamnati. kungiyar Manyan Ma’aikatan…

An karrama Shugaban Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC) da lambar yabo bisa kan shugabanci nagari wajen tafiyar da ma’aikatun gwamnati.

kungiyar Manyan Ma’aikatan Ma’aikatun Gwamnati (SSASCGOC) ce ta karrama shugaban don nuna gamsuwa da gudunmawar da shugaban yake bayarwa wajen sake fasalin harkokin sufurin jiragen ruwa, musamman ma kafa Tashar Teku-Huta ta Kaduna da sauran sassan kasar nan da kuma bullo da shirin inganta jin dadin ma’aikata da kyautata dangantaka a tsakanin ma’aikata da shugabannin Hukumar NSC.

Lokacin da yake amsar lambar yabon, Shugaban Hukumar NSC din wanda Daraktan Harkokin Abokan Hulda na Hukumar, Alhaji M.B. Abubakar, ya wakilta ya gode wa kungiyar kan lura da gudunmwar da yake bayarwa.

Ya sadaukar da lambar ga daukacin ma’aikatan Hukumar NSC, wadanda ya ce ba zai samu wata nasara ba, ba tare da gudumawarsu ba.