✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Hukumar FIFA zai yi ta-zarce a karo na biyar

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta duniya Mista Sepp Blatter ya bayyana aniyarsa ta yin ta-zarrce a karo na biyar a zaben Hukumar da zai gudana…

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta duniya Mista Sepp Blatter ya bayyana aniyarsa ta yin ta-zarrce a karo na biyar a zaben Hukumar da zai gudana a watan Mayun shekarar 2015.
Tun cikin shekarar 1998 ne dai Mista Sepp Blatter yake jagorancin Hukumar.
Shugaban ya ce ya yanke shawarar sake tsayawa takarar shugabancin hukumar ne bayan Shugaban Hukumar kula da kwallon kafa a Nahiyar Turai (UEFA) Micheal Platini ya bayyana cewa ba zai yi takarar neman shugabancin FIFA a badi ba.
“A wannan wata na Satumba ne nake sa ran sanar da duniya cewa zan sake tsayawa don yin takara a shugabancin hukumar a karo na biyar a taron da shugabannin hukumar za su yi a ranakun 25 da kuma 26 a hedkwatar hukumar da ke Zurich a Suwizilan”, inji Mista Sepp Blatter.
A watan jiya ne Mista Michel Platini ya bayyana cewa ba zai yi takarar shugabancin hukumar ba abin da ya kawo karshen rade-radin da wasu ke yi na Platini zai kalubalanci Blatter a zaben badi.
Idan Sepp Blatter ya samu nasarar sake darewa don shugabancin hukumar zai zama daya daga cikin wadanda suka fi dadewa suna yin shugabanci a hukumar.  Hakan zai ba shi damar shafe kimanin shekara 20 yana yin shugabanci.
A zamanin Blatter ne aka fara gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a karon farko a Nahiyar Afirka a kasar Afirka ta Kudu a shekarar 2010.