✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shugaban Gabon ya nada mace a matsayin Mataimakiyarsa

Rose ta zama mace ta farko da ta taba rike mukamin Mataimakin Shugaban Kasa a tarihin Gabon.

Shugaban kasar Gabon, Ali Bongo, ya nada Firamistar Kasar, Rose Christiane Ossouka Raponda, a matsayin mataimakiyarsa.

Da wannan, Rose ta zama mace ta farko da taba riki wannan mukamin a tarihin kasar.

Da kuma ita ce mace ta farko a kasar da ta taba rike mukamin Firaminista.

Kafin nadain nata, Roce ce Firaministar kasar, haka nan Ministar Tsaro.

Tsohuwar Ministar Tsaron, mai shekaru 59, wacce aka nada a mukamin Fira Minista a watan Yulin 2020 bayan wanda ya gabace ta ya yi murabus, yanzu ta zama mataimakiyar Shugaban Kasa duk da cewa mukamin bai ba da damar yin aiki na wucin-gadi a matsayin Shugaban Kasa ba.

Tuni dai Shugaban Kasar ya maye gurbin Rose da tsohon minista Alain-Claude Bilie-By-Nze, a matsayin sabon Firaministan kasar kamar yadda Babban Sakataren gwamnatin kasar, Jean-Yves Teale ya bayyna cikin bidiyon da aka wallafa a shafin Twitter na Shugaban Kasar.