Kotun Ƙoli ta soke hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta yanke wanda ya amince da Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar LP na ƙasa.
A ranar Juma’a, wani kwamitin alƙalai biyar na Kotun Ƙoli, ya ce Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta da hurumin yanke hukunci kan shugabancin jam’iyyar.
- APC ta ƙaryata jita-jitar sauya Shettima kafin zaɓen 2027
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta
Alƙalai sun bayyana cewa batun shugabanci al’amari ne da ya shafi cikin jam’iyya, kuma ba kotu ke da ikon yanke hukunci a kai ba.
Kotun ta kuma ce wa’adin mulkin Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar ya ƙare tun da farko.
Kotun ta amince da ƙarar da Sanata Ester Nenadi Usman da wani mutum suka shigar.
Sai dai ta yi watsi da ƙarar da ɓangaren Abure ya shigar, inda ta bayyana cewa ba ta da amfani.
Wannan hukunci na shugabancin Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar LP ya ƙare hukumance.