Shugaban Amurka Joe Biden ya yi barazanar sanya haraji a kan manyan kamfanonin man da suka ki rage farashinsu domin saukakawa jama’ar kasar kuncin da suke fuskanta.
Wadannan kalamai suna zuwa ne a daidai lokacin da manyan kamfanonin man kasar ExxonMobil da Chevron suka bayyana samun gagarumar riba sakamakon hauhawan farashin makamashin da aka samu saboda mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
- Shin dagaske dan Davido mai shekara uku ya mutu a ruwa?
- Matsalar Tsaro: Kalubale gareku ’yan sanda —Buhari
RFI ya ruwaito cewa cikin makamashin da farashin su ya tashi har da iskar gas sakamakon yadda kasashen Turai ke saye shi domin cike gibin wadanda suka saba samu daga kasar Rasha.
Kokarin shugaban na ganin kasashen da ke da arzikin mai da iskar gas sun kara yawan wadanda suke hakowa domin rage farashinsa a kasuwannin duniya ya ci tura, yayin da kasashen suka bijirewa kiran da Biden ya musu.
Shugaban Rasha Vladimir Putin da Yarima Salman na Saudiyya sun ki amincewa da kiran, yayin da ita ma Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur ta OPEC ta bijire.
Yakin Ukraine ya sa farashin makamashi ya tashi, a daidai lokacin da kasashen Yammacin Duniya suka takaita sayen mai daga Rasha.