Majalisar Dokokin Afrika ta Kudu ta kada kuri’ar kin amincewa da fara shirin tsige Shugaban Kasar, Cyril Ramaphosa daga mukaminsa.
Tun da farko dai an fara yunkurin tsige shi ne kan wani rahoto da ya nuna ya boye makudan kudin kasashen waje da bai bayyana ba a gonarsa a shekarar 2020.
- Najeriya ta cire dokar gwajin COVID-19 ga matafiya kwata-kwata
- NAFDAC ta kwace jabun magunguna na N20m a kasuwar Zariya
Sakamakon kuri’ar da aka kada ranar Talata, ya nuna ’yan majalisa 214 ne suka ki amincewa da shirin tsige shugaban, yayin da 148 suka yarda da hakan.
Galibin ’yan majalisar daga jam’iyyar ANC mai mulki sun nuna suna tare da Shugaba Ramaphosa, inda suka hana yunkurin samun kashi biyu bisa ukun da ake nema kafin a iya tsige shi.
Duk da haka, hudu daga cikin ’yan jam’iyyar ta ANC, sun kada kuri’arsu ne kan nuna goyon bayansu ga shirin tsige shugaban.
Bukatar kada kuri’ar ta taso ne bayan da rahoton majalisar ya yi zargin Shugaban ya boye tsabar kudi akalla Dalar Amurka 580,000 a wata gonarsa ba tare da ya sanar da ’yan kasar komai ba.
Wannan ya sa rahoton majalisar ya bukaci a kada kuri’a dangane da shirin tsige shugaban saboda abin da ya aikata.
Kada kuri’a na zuwa ne a daidai lokacin da Ramaphosa ke fafutukar sake neman zabe a matsayin shugaban ANC na kasa yayin babban taron jam’iyyar wanda za a fara gudanarwa ranar Juma’a, a birnin Johannesburg na kasar.