Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ke zaman jinya a Birnin Landan da ke kasar Ingila ya kira takwaransa na Saliyo Ernest Bai Koroma inda ya jajanta masa a kan bala’in da ya sauka a kasar.
Mai taimaka wa shugaba Buhari a kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne sanar da hakan inda ya ce Buhari ya yi wa shugaban kasar na Saliyo ta’aziyar wadanda suka rasa rayukansu a zaftarewar lakar. Sannan y ace ‘yan Najeriya baki daya ja jimamin abin da ya faru. Sannan kuma ya yi addu’ar Allah Ya ba wadanda suka rasa rayukansu hakurin rashin.
Shugaban kasar Saliyo ya nuna godiya da jin dadin yadda Buhari ya nuna rashin dadin abin day a faru a kaar, sannan ya yi addu’ar Allah Ya kara wa Buahri lafiya.