Gwamantin Tarayya ta ce kiraye-kirayen neman Shugaba Buhari ya yi murabus daga matsayinsa alama ce ta rashin sanin ya-kamata.
Ministan Yada Labarai, Kai Mohammed ya bayyana haka a lokacin ganawarsa da Kungiyar Masu Gidajen Jarida ta Najeriya (NPAN).
- Shekarau ya kalubalanci Buhari kan kin sauke manyan Hafsoshin Tsaro
- Kashe-kashe: Shaikh Gumi ya bukaci Buhari ya yi murabus
- A kori Fashola: Ba abin da ya yi a Arewa —NEF
Ministan ya ce neman Shugaba Buhari ya yi murabus saboda lalacewar sha’anin tsaro “shigar kazamar siyasa ce cikin al’amarin tsaro”.
A farkon makon nan ne Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta bukaci Buhari ya yi murabus bayan harin kungiyar Boko Haram da ta kashe manoma 43 a Zabarmari, Jihar Borno.
NEF ta zargi Buhari da rashin katabus wurin kawo karshen matsalar tsaro da kashe-kashe da suka addabi yankin Arewa.
“A kasashen da suka waye, duk shugaban da ya kasa samar da tsaro, sauka yake yi daga mukaminsa”, inji kakakin NEF, Hakeem Baba-Ahmed.
Ita ma kungiyar yankin Neja Delta (PANDEF) da Gamayyar Dattawan Najeriya kan Zaman Lafiya da Kyakyyawan Shugabanci (CONEPAGG) sun bayyana takaici kan tabarbarewar sha’anin tsaro a Najeriya.
Kiraye-kirayen babu fa’ida
Da yake magana kan harin Zabarmari da Boko Haram ta kashe sama da manoma 43, Lai Mohammed ya ce, “Bayan harin an yi ta neman Shugaban Kasa ya sauka daga mukaminsa.
“Wannan mummunan salo ne na sanya siyasa a sha’anin tsaro wanda babu dattaku a ciki.
“A 2015 an zabi Shugaban Kasa a wa’adi mai shekara hudu sannan a 2019 aka kara zaben shi a wani wa’adi na shekara hudu. Babu kiraye-kirayen da za su hana shi kammala wa’adinsa”, inji ministan.
Lai Mohammed ya ce gabanin mulkin Buhari Boko Haram na kai-komo da kai hare-hare yadda ta ga dama a garuruwan Arewa kamar Kano, Kaduna da Jos da sauransu.
“Yanzu ya zama tarihi wanda kuma ba bagatatan ba ne, sannan sojoji sun samu gagarumar nasara a lokacin mulkin Buhari.
“Saboda haka neman ya sauka daga mulki koma-baya ne ga yaki da ta’addanci; hakan ba komai ba ne face siyasa da neman kawar da hankalin gwamnati. Mu guji sa siyasa a lamarin tsaro.
“Yanzu an karya lagon Boko Haram, ba ta da katabus sai dai hare-haren raggwanci da take kai wa manoma kamar yadda ta yi a karshen mako”, inji shi.
Ya ce yanzu ta’addanci matsala ce da ta addabi duniya, sannan duk karfin ikon kasa, ba ta fi karfi a kai wa raunana hari a cikinta ba.
“Misali, karfin sojin Amurka wanda shi ne mafi karfi a duniya bai hana a kai mata harin 9-11 ba. Yanzu numfashin da kawai ya rage wa Boko Haram shi ne amfani da kafafen watsa labarai, shi ya sa suka yi sauri suka fitar da bidiyo cewa su suka kashe manoman.
“Harin Boko Haram a kan mutanen da ba za su iya kare kansu ba alama ce ta rauninta da kuma dagulewan al’amuranta, musamman a baya-bayan nan da suke kwasar kashinsu a hannu a wurin sojoji,” inji ministan.
Ba ma nadamar cewa Buhari ya sauka —NEF
A martaninsa ga kalaman Lai Mohammed, Kakakin NEF, Hakeem Baba-Ahmed ya ce neman Buhari ya ajiye mukaminsa bai saba wa tsarin dimokuradiyya ba.
“An zabi Shugaban Kasa ne domin ya yi wasu ayyanannun ayyuka ya kuma sauke wasu nauyi. Tun da ya gaza, mu kuma muna amfani ne da damarmu muna sanar da shi cewa ya kasa kuma babu dalilin ya ci gaba da rike mukamin”.