✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin tsaro: ‘Ba za mu miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba’

Tinubu ya yi kira da a nuna jajircewa wajen kare ikon Najeriya da kuma dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci sojoji da su ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar Najeriya yana mai jaddada alkawarin cewa ƙasar ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba.

Da yake jawabi ga sojojin a lokacin ziyararsa a Katsina, Shugaba Tinubu ya nuna damuwa game da ƙalubalen tsaron da ake fuskanta a ƙasar a halin yanzu, inda ya bayyana su a matsayin wani lokaci mai muhimmanci a tarihin Najeriya.

Tinubu ya yi kira da a nuna jajircewa wajen kare ikon Najeriya da kuma dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar.

Ya tabbatar wa sojojin da kudirinsa na kula da jin daɗinsu, inda ya yi alƙawarin biyan alawus-alawus a kan lokaci, tabbatar da kula da lafiya, da kuma tallafa wa iyalansu.

Ya jaddada jarumtaka da sadaukarwarsu, yana mai cewa su ne “garkuwar Najeriya.” Ya jaddada cewa yaƙin ba wai kawai na yankuna ba ne, har ma da yaƙin neman ran kasar.

Tinubu ya tabbatar da ƙudirin gwamnatinsa na tallafa wa sojoji da ayyuka da zuba jari, yana mai gargaɗin masu kawo cikas na cikin gida da na waje cewa Najeriya ba za ta miƙa wuya ba.

Ziyarar tasa ta kuma hada da ƙaddamar da titin mota mai hannu biyu mai tsawon kilomita 24 da cibiyar aikin gona ta zamani a Katsina.