Cibiyar Magance Rikice-rikice ta Kasa da Kasa (ICG) ta ce shirin Gwamnatin Najeriya na yi wa tubabbun mayakan Boko Haram da suka ajiye makamansu afuwa domin ba ya tasiri ko kadan.
ICG wata sanarwa ranar Alhamis ta bakin shugabanta, Robert Malley, ta zargi sojojin Najeriya da wasu wadanda babu ruwansu wajen yin katsalandan a cikishirin, wanda hakan a cewarsu ya sa tilas masu zuba kudadensu don ci gaban shirin suka ja da baya.
- Matan gwamnoni sun ba matan da aka yi wa fyade a Zamfara tallafi
- ’Yan sanda sun kwance wani abin fashewa a Kano
Kungiyar ta kuma zargi sojoji da azabtar da mutanen da ake zargi bayan sun fada hannun gwamnati, abinda ta ce yana haifar da tsoro ga wadanda suke shirin ajiye makaman nasu a nan gaba.
Kazalika, ta ce wanda suka tuba suka ajiye makamansu na fuskantar kalubale iri-iri daga ‘yan siyasa da sauran al’ummar Najeriya.
Daga nan sai kungiyar ta ce irin wannan tsaiko na kawo koma baya ga shirin na sauya tunanin tsoffin mayakan na Boko Haram.
Kungiyar ta ce dole ne sai gwamnatin Najeriya ta ba wa shirin gudunmawa ta musamman don samun cikakkiyar nasarar sanya su ajiye makamai domin su rungumi zaman lafiya.
A cewar ICG, shirin zai samu karbuwa ne kawai idan gwamnati ta inganta yadda ta ke tantance fararen hula da tsoffin mayakan da kuma inganta yadda ake horar da su domin sake mayar da su cikin al’umma.