Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa reshen Jihar Filato Alhaji Iliya Wushishi ya ce shirin dogaro da kai da kungiyar ta kirkiro zai taimaka wa al’umma su tsaya da kafafunsu.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da Wakilin Aminiya a garin Jos a ranar Litinin.
Shirin da aka kira ‘mannara’ ya kunshi taimaka wa jama’a da kudi da sauran hanyoyin taimako don al’umma su dogara da kansu.
Ya ce “Wannan shiri na ‘mannara’ wanda ake sayar da kati da ya kama daga Naira dubu 10 da na 5,000 da na 1,000 da na 500 da na 200 da kuma na Naira 100. Duk mai bukatar taimaka wa kungiyar sai ya sayi katin da zai taimaka ya kankare ya tura zuwa hedkwatar shirin da ke garin Kaduna.”
Ya ce idan aka ci gaba da bin wannan tsari batun kungiya ta tsaya tana taron neman gudunmawa don sayen wani abu ko kuma don gina wani abu zai rika tasowa ba.
Ya ce a karkashin wannan shirin kananan hukumomin da jihohi za su tsara ayyukan da za su gudanar na shekara da kuma kudin da aka tara su tura wa ofishin kungiyar na kasa.
Ya ce babu shakka ayyukan da kungiyar za ta gudanar a wannan shiri ba zai tsaya ga ’yan Izala kadai ba, zai amfani kowa da kowa ne a kasar nan. Don haka ya yaba wa shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau kan kokarin da ya yi wajen kirkiro wannan shiri.
Ya bukaci al’ummar Musulman Najeriya su ba wannan shiri goyan baya da hadin kai kasancewar shiri ne da zai taimaki al’ummar Musulmin kasar nan.
Shirin dogaro da kai da Izala ta kirkiro zai taimaka wa al’umma- Iliya Wushishi
Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa reshen Jihar Filato Alhaji Iliya Wushishi ya ce shirin dogaro da kai da kungiyar ta kirkiro…