✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shirin Allah domin fansar dan Adam (3)

A makon jiya, mun tsaya ne a kan mutuwar Yesu Almasihu da kuma tashinsa daga kabari; wadda ita ce tushen ban-gaskiyar dukan masu ba da…

A makon jiya, mun tsaya ne a kan mutuwar Yesu Almasihu da kuma tashinsa daga kabari; wadda ita ce tushen ban-gaskiyar dukan masu ba da gaskiya ga shirin Allah domin ceto. A yau, ina so ne mu kara ci gaba game da wannan shiri domin mu samu karin fahimta game da wannan asiri na Allah na ceto dan Adam. A cikin Littafin 1Korinthiyawa 2: 4 – 8, maganar Allah tana cewa “Maganata kuma da wa’azina ba tare da zantuttuka na hikima masu rinjayarwa ba ne amma da shaidar ruhu da iko: domin kada ban-gaskiyarku ta tsaya cikin hikimar mutane, amma cikin ikon Allah. Duk da haka muna maganar hikima a wurin cikakku: amma hikima ba ta wannan zamani ba, ba kuwa ta mahukuntan wannan zamani ba, da suke shudewa: amma muna maganar hikima ta Allah cikin asiri; wato hikima wadda take a boye wadda Allah Ya kaddara ta kafin farkon zamuna domin darajarmu. Hakiman zamanin nan kuwa duka ba su santa ba: gama da sun santa da ba su giciye Ubangijin daraja ba.” Me ya sa Shaidan yana ‘da na sani’? To da Shaidan ya ga kamar ya ci nasara a kan Yesu Kiristi, da yake ya sa an kashe shi, an kuma sa shi cikin kabari; ba ma kawai kabari ba; amma shi Shaidan ya sa an sa masu tsaro a bakin kabarin domin ba ya son a sace gangar jikin Yesu Kiristi. Duk da wannan ‘kyakkyawan’ shiri da ya yi, kabari bai isa rike shi ba, mutuwa kuma ba ta da iko a bisansa. A yau mun san cewa ya tashi daga matattu domin mu, mu samu rai. Tashin Yesu Kiristi daga matattu ya lalatar da ikon Shaidan gaba daya. Tun farkon halita, Allah Ya ba mutum ikon mulki bisa wannan duniya. Yayin da Allah Yana mulki bisa komai da kowa; sai Ya ba mutum ikon shugabancin duniyar nan. Sa’adda mutum ya ci gaba da tafiya cikin biyayya, Allah Yana tare da shi kuma yana da cikakken iko bisa kowane halittar Allah. Shi Iblis ba ya son wannan ta kasance, shi ya sa ya zo domin ya rudi mutum, ya yi wa Allah rashin biyayya; da zarar mutum ya ki bin umarnin Allah, ya aikata abin da Allah Ya ce kada ya yi, ragamar mulki da Allah da kanSa Ya damka masa: ya dauka ya mika wa Shaidan ta wurin rashin biyayya. Tun daga wancan lokacin har ranar da Yesu Almasihu ya tashi daga kabari; Shaidan ne ke da mulki a bisa wannan duniya da abin da ke faruwa ciki kuma. Abin da bai sani ba shi ne, mutuwar Yesu Almasihu shi ne ya kwato ’yancin mutum daga bautarsa da kuma bautar zunubi. Abu na biye kuwa shi ne, ta wurin mutuwar Yesu Almasihu har mu ma mun ci nasara bisa shi Shaidan da duk sauran masu aiki da shi. Maganar Allah na koya mana cewa: “Da shi ke fa ’ya’ya masu tarayya ne cikin jini da nama, shi kuma da kansa ya dauki tarayya da su cikin wadannan domin ta wurin mutuwa shi wofinta wanda yake da ikon mutuwa wato Shaidan: shi kuma sake dukan wadanda ke karkashin bauta muddar ransu saboda tsoron mutuwa.” (Ibraniyawa 2 : 14 – 15). Haka nan kuma a cikin Littafin Kolosiyawa 2 : 6 – 15, maganar Allah na koya mana cewa: “Tun da shi ke kun karbi Kiristi Yesu Ubangiji, sai ku yi tafiya a cikinsa haka nan, dasassu, ginannu kuma cikinsa, kafafu cikin ban-gaskiyarku, kamar yadda aka koya maku, kuna yalwata cikin godiya. Ku yi hankali kada kowa shi same ku ta wurin iliminsa da rudinsa na banza, bisa ga tadar mutane, bisa ga rukunai na duniya ba bisa ga Kiristi ba: gama daga cikinsa dukan cikar Allahntaka cikin jiki tana zaune, cikinsa kuwa an kamilta ku, shi wanda shi ke kan dukan mulki da iko: a cikinsa kuma aka yi maku kaciya da kaciya wadda ba hannu ya yi ba, cikin tubewar jikin nama, cikin kaciya ta Kiristi; biznannu ne ku tare da shi cikin baptisma, inda aka tashe ku tare da shi ta wurin ban-gaskiya cikin aikin Allah, Wanda Ya tashe shi daga matattu. Ku kuma, da ke matattu ta wurin laifuffukanku da rashin kaciya na namanku, ku ne ke cewa, ya rayadda ku tare da shi, ya kuwa gafarta maku dukan laifuffukanmu, ya shafe shari’a wadda ta tsaya mana bisa ga farillanta, tana kuwa gaba da mu: ya kawar da ita daga turba, yana kusance ta ga giciye; bayan da ya tube ma kansa mulkoki da ikoki, ya nuna su a sarari, yana kusance ta ga giciye.” Dole ne Shaidan ya ce ‘da na sani’; domin kuwa dukan hujjar da ya ba shi bisa mutum; Allah, ta wurin mutuwar Yesu Kiristi ya kawar da su gaba daya. A yau, ta wurin zubar da Jinin Yesu Kiristi, Allah Ya wanke dukan zunuban wanda ya ba da gaskiya gare shi. Bisa ga maganar Allah cikin Littafin Ishaya 53 : 1 – “ Wane ne ya gaskanta abin da muka ji? Ga wane ne kuma hannun Ubangiji Ya bayyyana? Gama ya yi girma a gabansa kamar dashe mara kwari, kamar saiwa a cikin busasshiyar kasa: ba shi da wani fasali, ba kuwa dadin gani gare shi; sa’anda mun dube shi, ba wani jamali gare shi da za mu so shi ba. Abin raini ne, yasashe ne a wurin mutane, mai bakin ciki ne, ya saba da ciwuta, aka rena shi kamar wanda mutane suka kawar masa da fuska, mu kuma ba mu maishe shi wani abu ba. Lallai da kayan ciwutanmu ya nawaita, ya dauki bakin cikinmu; amma muka maishe shi bugagge, dukakke na Allah, mai shan wuya ne. Amma sabili da laifuffukanmu ne aka yi masa rauni, aka kuje shi domin kura-kuranmu; horo kuma mai kawo lafiyarmu a kansa yake, ta wurin dukansa da ya sha mun warke. Dukanmu kamar tumaki muka bata; kowane dayanmu ya karkata garin bin nasa tafarkin; Ubangiji kuma Ya dibiya masa dukan kura-kuranmu. Aka wulakance shi, duk da haka ya yi tawali’u, ba ya bude bakinsa ba, kamar dan rago da aka kai wurin yanka, kamar yadda tunkiya wurin masu sosayanta tana shiru, haka nan ba ya bude bakinsa ba. Bisa ga rashin gaskiya a shari’a aka kawar da shi: don mutanen zamaninsa fa, wane ne a cikinsu ya lura aka datse daga kasar masu rai? Sabili da laifuffukan mutane na aka buga shi ………..Amma Ubangiji Ya nufa a kuje shi, Ya sa masa azaba: lokacin da za ka maida ransa hadaya domin zunubi, za ya ga zuriyarsa, za ya tsawanta kwanakinsa, nufin Ubangiji kuma za ya yi albarka a cikin hannunsa. Za ya ga wahalar ransa, zuciyarsa za ta kwanta kuma: ta wurin saninsa kuma bawana mai adalci za ya baratar da masu yawa, za ya dauki kura-kuransu kuma.”