Abokin takara na wucin gadi wanda a turance ake kira Dummy running mate, mutum ne da yake a matsayin wanda zai zame wa tsayyayen dan takara mataimaki na wuci gadi ko kuma na rikon kwarya a karkashi tikiti daya na takarar mukamin wata kujera ta siyasa.
Sai dai galibi ana amfani da wannan jumla ce ta Dummy running mate idan kujerar da ake takara a kanta ta Shugaban Kasa ce, sai ya zamana mai takarar Kujerar Mataimakin Shugaba Kasa a karkashin wannan tikiti na jam’iyya daya, ana kiransa da abokin takara na wucin gadi.
- An yi wa maniyyatan Kano bitar Aikin Hajji a aikace
- Zaben Gwamnan Ekiti: Ranar Asabar Fayose da Fayemi za su sake gwada kwanji
Misali, a yanzu dai jam’iyyar APC ta tsayar da tsohon gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu a matsayin dan takararta na kujerar Shugaban Kasa na Zaben 2023.
Jam’iyyar ta tsayar da Tinubun ne a yayin Babban Taronta na zaben fitar da gwani da ta gudanar a tsakanin ranar 7 zuwa 8 ga watan Yunin da muke ciki.
Sai dai tun daga wannan lokaci, jam’iyyar ta gaza cimma matsaya, inda ta rika fadi-tashin ganin ta zabi abokin takarar Tinubun amma hakarta ba ta cimma ruwa ba har zuwa lokacin da wa’adin mika sunayen ’yan takara ga Babbar Hukumar Zabe ta kasar ya cika.
A yayin da wa’adin ke cika ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Yuni, jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta mika sunan wani jigon dan siyasa daga Jihar Katsina, Alhaji Kabiru Ibrahim Masari a matsayin wanda zai yi wa Bola Tinubu abokin takarar Shugaban Kasa na wucin gadi.
Wannan dai na zuwa ne a sakamakon rashin cimma matsaya da jam’iyyar APC ta yi bayan cikar wa’adin da Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta bayar na mika sunayen ‘yan takarar kujerar Mataimakin Shugaban Kasa.
Ana amfani da abokin takara na wucin gadi ne a wani dan kayadadden lokaci domin cimma wata bukata, ko kuma bude wata kofar warware wasu batutuwa a cikin jam’iyya gabanin ta tsayar ko kuma ta zabi abokin takararta na hakika.
Duk da cewa Dokar Zabe ba ta fito karara ta yi tanadin wannan dama ba ta tsayar da abokin takara na wucin gadi, sai dai tsari ne na cikin gida da a siyasa bai haramta wanda jam’iyya ke yi a bayan fage.
Sai dai kuma babu shakka Dokar Zaben ta yi tanadin cewa kowacce jam’iyya za ta iya sauya dan takarar da tsayar, saboda haka jam’iyyu suna da damar da za su yanke shawarar gabatar da abokin takara na wucin gadi, daga bisani kuma su sauya shi matukar wa’adin da Hukumar INEC ta bayar na sauya dan takara bai cika ba.
A irin wannan yanayi ya sanya jam’iyyar APC kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar, ta tursasa wa Alhaji Kabiru Masari cike wata takarda mai dauke da yarjejeniyar cewa zai fito ya bayyana cewa ya janye takararsa gabanin wa’adin da doka ta tanada ya cika.
Sai dai hadarin gabatar da abokin takara na wucin gadin shi ne, muddin ya zamana ba a yi taka tsantsan ba wajen bin duk wasu matakai gabanin kulla yarjejeniyar wannan tsari na bayan fage, akwai yiwuwar wanda aka tsayar din ya yi buris ya ki janye wa wanda jam’iyyar take son tsayarwa a matsayin abokin takararta na hakika.
Hakan kuma zai sa abokin takarar ya zame wa jam’iyyar tamkar wani alakakai ko kuma takalmin kaza.