A safiyar ranar Juma’a 1 ga watan Maris ɗin shekarar 2024, aka wayi gari da rahoton murabus ɗin Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Fitaccen malamin na addinin Musulunci ya sanar da ajiye muƙamin nasa ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Sheikh Daurawa ya ɗauki matakin ne kwana guda bayan Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya soki Hukumar Hisbah bisa salon ayyukanta waɗanda ya ce suna keta doka.
Sheikh Daurawa ya ce gwiwoyinsa sun yi sanyi bayan da ya saurari kalaman gwamnan kan sukar da ya yi wa Hukumar Hisbah.
Sai dai a jawabin Sheikh Daurawa, ya bai wa gwamnan haƙuri sannan ya bayyana cewa ya sauka daga muƙaminsa.
“Mun yi iya kokarinmu, mu ga cewa muna abin da ya kamata, to amma ina ba mai girma gwamna hakuri bisa fushi da ya yi da maganganun da ya faɗa.
“Kuma ina rokon da ya yi min afuwa, na sauka daga wannan mukami da ya ba ni na Hisbah, inda muka yi kuskure muna fata a yafe mana. Kuma ina yi masa masa addu’a da fatan alheri.”
Kalaman Gwamnan Kano kan ayyukan Hisbah
A ranar Alhamis ne Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya gargadi Hukumar Hisbah da ta rika taka-tsan-tsan wajen kiyaye hakkin dan Adam a yayin aiwatar da ayyukanta.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a wani ɓangare na jawaban da ya gabatar yayin ganawa da malamai a Fadar Gwamnatin Kano.
Gwamnan wanda ake yi wa lakabi da Abba Gida-Gida, ya bayyana damuwarsa kan wani bidiyo da ya ce ya yi arba da shi kan yadda Hukumar Hisbah ke gudanar da ayyukanta wajen kama wadanda ake zargi da aikata laifuka masu nasaba da badala.
A yayin taron wanda Abba Gida-Gida ya yi wa malamai nasihar lura da nauyin da rataya a wuyansu, ya bayyana cewa ya ga wani bidiyo jami’an Hisbah suna cicciba ’yan mata da samari ana dorawa a mota da sunan gyara.
A cewarsa, “Hisbah Hukuma ce mai albarka wadda muka dauka da martaba, kuma muka ɗauko bayin Allah wanda muka san za su iya muka ce ga amanar al’ummar Jihar Kano.
“Amma ma’anar Hukuma shi ne ta yi abin da ya ke daidai kuma a bai wa Gwamnatin shawara sannan a samu hadin kai tsakanin Gwamnati da masu ruwa da tsaki.
“Na ga wani bidiyo da ya tayar min da hankali, kira nake da jan hankali gyara muke so.
“An ɗebi motoci, an je inda wasu matasa ke ɓarna maza da mata, amma yadda aka riƙa debo su ana duka da gora, suna gudu ana bi, ana tadile kafafunsu, ana debo su kamar awaki haka a jefa su a cikin Hilux.
“Wani ma Allah Ya kiyaye in kashin bayansa Spinal Cord ya karye ya gama yawo har abada.
“Wannan muna ganin kuskure ne babba, ka rungumo matashiya ko matashi ka jefa shi kamar akuya a cikin Hilux.
“Na ga bidiyo da aka je inda ɗaliba a Jami’ar Bayero suke har inda suke har dakunansu ana duka ana rungumosu, ana jefa su a cikin mota.
“Mu muna ganin akwai gyara. Mun saka hukuma saboda ta yi wa addini musulunci hidima, amma idan aan irin wannan to yaran ma sai su kangare, abin da ake so su yi na gyaran sai a samu akasin haka. Allah Ya kiyaye.
“Idan yaran nan suka kangare mana a Jihar Kano, yaya za mu yi da su? Amma a fita da motoci, a fita da jami’an tsaro, a hada da Hisbah, a hada da ’yan sanda, a hada da Sibil Difens, amma ba ma so a hada da sojoji, don idan aka hada da soja ta baci.
“A je da SS, duk inda aka san ana wannan aiki marar kyau, a je a kamo wadannan yara ko wadannan mutane a danka su a hannnun hukuma, don Allah Yana son ka kare mutuncin dan Adam dan uwanka,” inji Gwamnan.
Takaddamar Murja da Hukumar Hisbah
Kamar yadda rahotanni suka nuna, a ’yan kwanakin nan batun Murja ya ja hankalin kusan kowa a Jihar Kano da ma kewaye, bayan da Hukumar Hisbah ta kama ta amma kotu ta ba da umarnin a sake ta, lamarin da bai yi wa Daurawa daɗi ba.
Ga dai wasu lokutan da takaddamar Murja da Hisbah ta wakana:
A farkon watan Nuwambar 2023, Hukumar Hisbah ta gayyaci matasa – mata da maza masu amfani da shafin TikTok ciki har da Murja don yi musu nasiha kan yadda ake zargin wasu daga cikinsu wajen ɗabbaƙa ayyuka na baɗala.
A ranar 24 ga watan Janairun 2024, Hukumar Hisba ta sanar cewa tana neman wasu ‘yan TikTok shida ruwa a jallo ciki har da Murja Kunya bisa zargin su da wallafa bidiyo masu ɗauke da kalamai na batsa.
A ranar 13 ga watan Fabrairun 2024, Hisbah ta kama Murja da abokin hulɗarta kamar yadda Babbar Mataimakiyar Kwamanda Hisbah Dokta Khadija Sagir Suleiman ta sanar.
An kuma tura Murja gidan gyaran hali don jiran ranar 20 ga watan Fabrariru da za ta sake bayyana a gaban kotun, lamarin da Murja ta musanta tuhume-tuhumen da ake mata.
A ranar 18 ga watan Fabrairun 2024 aka saki Murja — kwana biyu gabanin ta sake bayyana a gaban kotu domin ci gaba da sauraren shari’arta.
Hakan ya haifar da ce-ce-ku-ce kan yadda aka saki fitacciyar ‘yar Tiktok din. Amma hukumar gidan gyaran hali ta Kano ta ce kotu ce ta ba da umarnin a sake ta.
Sheikh Daurawa ya fito ya nuna rashin jin dadinsa kan sakin Murja inda ya yi nuni da cewa, “wanda ya fi karfin dokar Hisbah, ai bai fi karfin ta Allah ba.”
A ranar 20 ga watan Fabrairu, kotu ta ce a yi wa Murja gwajin lafiyar kwakwalwa duba da irin halayyar da ta nuna a lokacin zaman kotun da aka yi da ita da farko.
A ranar Alhamis 29 ga watan Fabrairu, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya soki yadda Hukumar Hisba take kama matasan da ake zargi da aikata ayyukan baɗala bayan wani bidiyo da ya ce ya kalla – bidiyon da ya ce “ya tayar masa da hankali.”