Manjo-Janar Muhammad Inuwa Idris mai ritaya, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman na Jihar Kano, ya yi murabus.
Wannan dai na zuwa ne bayan shafe watanni bakwai kacal da karɓar muƙamin.
- Rikicin Masarauta: Duk mai ja da hukuncin Allah ba zai yi nasara ba — Sanusi II
- DAGA LARABA: Yadda Farashin Kayan Masarufi Suke Gabanin Sallah
Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Kano, Mustapha Muhammad ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Larabar.
Sanarwar ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus ɗin Kwamishinan yana kuma yaba masa kan ƙwazon da ya yi wajen sauke nauyin da aka ɗora masa.
Kazalika, gwamnan yana yi wa Manjo-Janar Idris fatan samun nutsuwa da kwanciyar hankali a ritayar da ya yi.
Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar 16 ga watan Agustan bara ne aka rantsar da Manjo-Janar Muhammad Inuwa a matsayin kwamshinan, amma sai kimanin watanni biyar da suka gabata ne aka ƙirƙiro sabuwar ma’aikatar wacce aka danƙa ragamarta a hannunsa.