Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi na al’ada a faɗin Jihar Kano.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ya fitar a wani taron manema labarai da ya gudana a hedikwatar rundunar da ke Bompai a wannan Juma’ar.
- Ɓarayin kekunan ɗinki sun shiga hannu a Borno
- ECOWAS ta gyara cibiyar magance shan miyagun ƙwayoyi a AKTH
CP Bakori ya ce hakan na cikin shawarwarin tsaro da rundunar ta bai wa mazauna jihar gabanin bukukuwan ƙaramar sallah da za a soma ranar Lahadi ko Litinin.
Sanarwar ta ce rundunar za ta baza jami’anta a sassan jihar domin tabbatar da bin doka da oda a jihar, kafin sallah da lokacin bukukuwan bayan sallar.
“Haka kuma an haramta duka nau’ikan hawan sallah da duk wata kilisa ta dawakai ko tseren mota a lokacin bukukuwan sallah ƙaramar da ke tafe,” in ji sanarwar.
’Yan sandan sun ce sun ɗauki matakin ne sakamakon rahotonnin tsaro da suka samu da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, domin tabbatar da zaman lafiyar al’ummar jihar.
Haka kuma ’yan sandan sun shawaraci mazauna jihar da su gudanar da sallar idinsu cikin kwanciyar hankali da lumana, yadda aka saba, ba tare da tashin hankali ba.
“Don haka muna kira ga al’umma da su kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa”, in ji sanawar.
Hakan na zuwa ne dai bayan da jama’a suka zura ido suna jiran ganin Sarki Muhammadu Sanusi II zai yi hawan sallah a jihar, bayan Sarki Aminu Ado Bayero ya sanar da janye hawan saboda dalilai na tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Ko a bara ma dai sai ’yan sanda suka haramta hawan Sallah a birnin na Dabo a sakamakon taƙaddamar masarautar jihar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.