✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aminu Ado ya soke hawan salla don gudun rikici a Kano

Ya ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero, ya soke shirinsa na gudanar da bikin hawan salla bayan shawarwari da dattawa da malaman addini suka ba shi.

Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan buƙatar tabbatar da zaman lafiya a jihar, biyo bayan shiga ruɗani da jama’a suka yi.

Wannan na zuwa ne yayin da aka shiga ruɗani a Kano saboda rikicin masarauta, biyo bayan mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Tun farko, duka sarakunan biyu – Sanusi II da Aminu Ado Bayero, sun shirya gudanar da hawan salla, lamarin da ya haddasa fargaba a tsakanin al’umma.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Laraba, Sarki Aminu, ya ce ya ɗauki matakin ne bayan jin ra’ayin malamai da dattawa.

“Malamai da dattawa sun shawarce mu, kuma muna mutunta su. Don haka, bayan nazari tare da majalisar masarauta, mun yanke shawarar cewa mun janye domin zaman lafiya,” in ji shi.

Idan za a tuna, a makon da ya gabata ne, Aminu Ado, ya aike wa ’yan sanda takardar neman izinin gudanar da hawan salla, bayan da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci Muhammadu Sanusi II, ya shirya yin hawan salla a bana.

Sarkin ya jaddada cewa bikin hawan salla ba abu ne da ya zama wajibi ba idan zai iya haddasa rikici da asarar rayuka.

“Idan akwai fargabar cewa hawan salla zai haddasa tashin hankali da asarar rayuka ko dukiyoyi, to, yana da kyau a daina,” in ji shi.

A gefe guda, al’ummar Kano sun nuna damuwa kan yadda rikicin masarautar ke ci gaba da yin tasiri a rayuwarsu.

Ana sa ran wannan matakin zai rage fargabar da ake ciki, tare da tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kano.