✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shin Peter Obi zai hade da Atiku?

Ya ce wannan batu ne mara tushe balle makama

Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi, ya ce babu wata tattaunawa tsakaninsa da takawaransa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, don hadewa.

Babban jami’in yada labarai na Kwamitin Yakin Neman Zaben Obi, Diran Onifade ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Laraba.

“An matsa mana da tuntuba game da tattaunawa da ake zargin na gudana tsakanin dan takararmu da na PDP, Atiku Abubakar.

“Muna sake jaddadawa kamar yadda muka fada da farko, wannan batu ba gaskiya ba ne, zance ne mara tushe.

“Babu wata tattauna da muke yi da Atiku ko waninsa da nufin janyewa daga takarar da muke yi.”

Ya kara da cewa Peter Obi ya shiga takara ne domin ya lashe zabe inda galibin ’yan kasa ke sa ran samun sabuwar Najeriya ’yantacciya daga karya da rashawa.