An kirkiro Jihar Kano ce a 1967 kuma a da birnin Kano yana cikin mashahuran birane tun tale-tale wato lokacin kasuwancin sahara.
Kano tun shekaru aru-aru babbar alkarya ce wacce dukkan kasashen Arewa yawancinsu na fararen fata wato a takaice Larabawa na Arewacin Afirka, kamar su Libya da Tunisiya da Aljeriya da Moroko da burinsu su shigo kasar Kano domin yin kasuwancin irin na da.
Ko da ni da nake da karamin karni na shekaru daga 1958 zuwa 1964, na ga Abzinawa suna kawo kayayyaki kamar kanwa da manda da zuma da sauransu, su kuma su zo da kudaden kasashensu a yi musu canji a nan su shiga Kantin Kwari domin sayen akoko wanda ake rina musu su yi kayansa su koma kasashensu, kususan Nijar da Mali tunda suna sahara, amma sun fi son kaya bakake.
Gaskiya unguwarmu Zango tana daya daga cikin wuraren da Buzaye suke sauka kuma da rakumansu har su samu lokaci mai tsawo a gidan mai saukarsu wato mai unguwa.
Ka ga tun wancan lokaci abin ambato da ma Kano yanzu da take da kananan hukumomi 44 ta shahara wurin karbar baki, kuma cikin ikon Allah har gobe da jibi ita ce take rike kowa naka.
Na san dai ba ma ’yan uwa bakar fata ba, hatta fararen fata a 1940 zuwa 1970 sun samu gurbin kasuwanci daga nan ne aka samu Kantin Kwari, wanda a da Kwarori ne daga Lebanon suka yi dandazo a wurin kuma yanzu ’yan kasa yawancinsu daga makwabtan Kano, kamar Katsinawa wadanda suka dade wurin kasuwanci tun kafin mu zo duniya, haka akwai Sakkwatawa dukkansu ’yan uwa ne na jini duk da jihohinmu daban-daban, amma dai shekaru masu yawa ana tare kuma an yi arziki sosai.
Kano ta kunshi mutane da yawansu ya kai da wuya a kididdige su cikin kankanin lokaci, amma dai sun fito daga Gabas da Yamma har da Kudancin kasar nan, kuma sun samu zaman lafiya da wadata, ba tare da kuntata wa kowa ba, ko kyashin abin da mutum ya mallaka.
Abu ne mai wahala Kanawa su sa ido ga abin arziki da wani bako ya mallaka. A takaice Allah Ya ba jama’ar Kano baiwar son baki kuma babu gori ko kyashi kamar yadda a yanzu wasu wurare ake kyamar baki har ma da a nan Arewa!
Abin da ba a gane ba, duk inda ake kin yaduwar baki za ka ga komai ya tsaya cak, babu albarka.
Dauki Birnin Madina Mai tsarki, za ka samu kowa cikin kaunar kowa, wannan ya faru shekara fiye da dubu da 400 kuma ko yau in ka je haka abin dai yake babu canji.
Sanin haka ne ya sa Kanawa da jiharsu ta Kano suka rungumi kowa ya zamo nasu kuma an ga haduwar arziki a ko’ina, kususan daga shekarar 2015 zuwa 2022, za ka iske irin ci-gaban kasuwanci da ginegine irin na Landan da Dubai.
Duk da dai masu kyashi suna tofa yawun kiyayya domin bakin cikin ba su suka kawo ci-gaban ba!
Mai karatu zai ga taken makalar na da ayar tambaya ce ganin an sa mutanen Kano a gaba kususan attajiri Aliko Dangote da Akanta Janar na Tarayyar Najeriya, wanda ake ta yi masa terere kawai saboda ana zarginsa da abin da har yanzu zargi ne ba a tabbatar ba, amma ana ta yada karya bisa wannan taliki.
Shin wannan Akanta Janar na Tarayya shi ne Ministan Kudi ko shi ne Gwamnan Babban Bankin Najeriya?
Babu daya kuma dole a yi bincike kafin bata wa wannan dattijon arziki suna kawai saboda zargi marar madafa.
Shi kuma Dangote ana cewa ya karye. A ina ya karye? Lallai Kano ta tsole wa wadansu idanu.
Kwamared Ibrahim Abdu Zango , shi ne Shugaban Kungiyar Kano Unity Forum da ke Kano za a iya samunsa ta tarho: 08175472298