A watan Satmban 2021 ne Gwamnatin Kano ta sanar da haramta nunawa ko sayar da fina-finan Hausa masu tallata dabanci, garkuwa mutane ko kwacen waya ko ta’ammali da miyagun kwayoyi a fadin jihar.
Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, Isma’il Naabba Afakallah, ya ce manufar haramta nau’ikan fina-finan ita ce kawar da yiwuwar matasan Kano su koyi aikata miyagun laifuka a dalilin kallon fim.
- A Kannywood ne zaka ga ’ya’yan da iyayensu suka kasa kula da su – Sarkin Waka
- Wata Sabuwa: Sauya jaruma a shirin Alaka ya jayo ce-ce-ku-ce
“Ba kowane matashi ne ke da hankalin fahimtar sakon da ke cikin kirkirarrun fina-finan ba; Wani zai iya dauka da gaske ne, ya je ya aikata irin abin da ya gani a ciki; Saboda haka ya zama wajibi mu dauki mataki tun ba mu makara ba”, inji Afakallah.
Ba ma biyayya ga son zuciya
Ya ci gaba da cewa, “Doka ta kafa ta, bai kamata mutum ya ajiye doka ba ya yanke hukunci musamman ma ba tare da zama da masu ruwa da tsaki ba.”
A lokacin ne aka fara rade-radin Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da fim din ‘A Duniya’, wanda hakan ya san furodusan fim din, Tijjani Asase, ya fito ya karyata batun.
A lokacin ya wallafa wani bidiyo, inda a ciki ya ce, “kamar yadda wasu mutane makaryata suke cewa wai an dakatar da fim din A Duniya, ba gaskiya ba ne. Fim din A Duniya yana nan ana ci gaba da aiki kamar yadda aka saba.
“Kuma bisa bin doka da oda na Hukumar Tace Fina-finai, muna tare da bin doka ta kasa da ta jiha a ko da yaushe.”
Ya kara da cewa, “Gwamnatin Tarayya ta haramta a nuna wani azzalumi a fim ba tare da an nuna hukuncin da aka yi masa ba.”
Asase ya kara da cewa ana shirya wasu abubuwan ne a fim domin a karshe a nuna karshen mai irin wannan halaye.
A lokacin masu ruwa da tsaki da dama a masana’antar ta Kannywood sun nuna rashin jin dadinsu kan lamarin.
Farfado da dabanci a fina-finan Hausa
An dade ana nuna dabanci a fina-finan Hausa, kuma an yi jarumai da dama da suka yi fice a harkar daba.
An yi jarumai irinsu Shu’aibu Lawal Kumurci da Tijjani Asase da Auwal Isa West da Aminu Shareef Momoh a baya.
Sai dai da kusan dukansu sun rage fitowa a rawar, inda suka hadawa da wasu bangarorin domin samu damarmaki da yawa.
Misali Aminu Momoh bai cika ma fitowa yanzu a irin wannan rawar ba, sai jefi-jefi, haka shi ma Tijjani Asase da Kumurcin.
A wata tattaunawa da Aminiya ta yi ba Ibrahim Meku, wanda shi me jarumi ne da ke fitowa a irin wannan bangare, ya ce yana jin takaicin yadda ba a ba su muhimmanci kamar sauran abokan aikinsu.
A lokacin da aka fara komawa YouTube da harkar fina-finai, musamman a lokacin kullen Kwarona, sai fim din Haram ya fara tashe.
A fim din, Adam Abdullahi Adam ko Daddy Hikima wanda aka fi sani da Abale a yanzu, shi ne ya fito a matsayin Ojo, inda a ciki abokin hamayyarsa, Sa a yi ma, ya yi garkuwa da mahaifiyarsa, sannan ya kashe ta.
Daga baya shi ma Ojo din yana garkuwa da diyarsa, sannan ya kashe ta.
Ana cikin haka ne aka fara nuna fim din A duniya, na Tijjani Asase, inda Daddy Hikima ya fito a matsayin Abale.
A fim din ne Abale wanda a baya yanayin aikace-aikacensaa masana’antar Kannywood ya sa ba a san shi ba sosai a baya, kasancewar aikin nasa na cigaban shiri da tsara wajen daukar fim duk ayyuka ne na bayan fage sai ya fara shuhura.
Kan ka ce kwabo, matasa suka fara rububin neman fim din suna kallo, sannan fim din ya zama abin magana a tsakanin matasa.
Daddy Hikima wanda haifaffen Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano ne, ya yi karatun boko har zuwa matakin zama nas a Kwalejin Kiwon Lafiya (ta Hygiene) da ke Kano bayan ya yi sakandare a Dawakin Tofa.
Komawa dabanci a fina-finan Kannywood
Haka bayan fitowarsa, sai ya zama kusan kowane furodusa yana nemansa domin ya yi aiki da shi.
Ganina yadda Abale ya samu karbuwa, sai masu shirya fina-finan Kannywood suka fara nema masa gurbi a duk fina-finansu.
Ko a shirin Labarina ya samu gurbi, sannan ya fara haskawa a tallace-tallace musamman na Kamfanin Bashir Maishadda.
Hakan ya sa Abale ya shirya nasa fim din mai suna Sanda, wanda nan ma ya samu karbuwa kuma na fada ne.
Akwai sabon fim din Dauda Kahutu Rarara mai suna Gidan Dambe, wanda Daddy Hikima ne fuskar fim din.
Akwai kuma fina-finai irinsu Uku sau uku da Asin da Asin da duk akwai fada a ciki.
A cikin fina-finan Kannywood da ake nunawa a YouTube masu dogon zango, babu wanda ya kai Izzar so samun masu kallo, wanda ba ya rasa nasaba da yanayin zamantakewa da ke ciki, sannan da yawa daga cikin masu kallon fim din sun ce ‘akwai Tauhidi a ciki’.
Sai dai masu shirya fim yanzu haka sun fara shirya fim din Tsayin Daka, wanda shi ma za a nuna a tashar Bakori TB din.
Sai dai maimakon yadda aka yi Izzar So, Tsayin Daka fim ne na fada, kuma an sa Abale a ciki tare da Lawal Ahmad.
Matasa na koyi da dabancin?
Binciken Aminiya ya gano matasa da dama sun tasirantu da wasu abubuwa da suke wakana a fina-finan.
Misali yanzu gaisuwar matasa musamman ‘’yan na’u’ sukan yi amfani da kalmar ‘In da Rabbana’, sai a amsa da ‘Ba wahala’ gaisuwar da har malamai sai da suka yi magana a kanta.
Haka kuma akwai gaisuwar daga hannaye sama su ratsa tsakaninsu da shi ma a irin fina-finan ka aka koya.
Sannan ana amfani da wasu salon maganganu da aka jiyo a fina-finan.
Sai dai binciken Aminiya bai gano wani matashi da ya fara shayeshaye da sare-sare saboda fim din ba.