✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shin da gaske an haramta yin tashe a Kano?

Rahotanni sun bayyana cewa, rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta haramta wani sabon salo na al’adar nan ta wasannin tashe da aka saba yi…

Rahotanni sun bayyana cewa, rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta haramta wani sabon salo na al’adar nan ta wasannin tashe da aka saba yi duk lokacin watan Azumin Ramalana.

Rundunar ta ce akwai bata-gari da ke fakewa da wannan al’ada wajen yi wa mutane sace-sace da kwace-kwace gami da dasa wawa a kan kayan da ba nasu ba.

Ta ce ba za ta lamunci a gudanar da irin wannan mummunan nau’i na al’ada ba kamar yadda ta kasance haramtacciya tsawon shekaru biyu da suka gabata inji wata sanarwa da kakakinta, DSP Abdullahi Kiyawa ya bayyana a ranar Laraba.

DSP Kiyawa ya ce, “ba wai duka tashe muka hana ba, wannan daman dole ne yara su yi wasanninsu na al’ada kamar yadda suka saba a lokacin azumi.

“Akwai wani irin nau’i na tashe da ake yi wanda shi na daban ne, za ka ga ’yan daba sun fito suna yi wa mutane kwace, to irin wadannan nau’ikan tashen ne aka hana.

“Domin kuwa mu abin da ba za mu lamunta ba shi ne yadda wasu bata-garin matasa ke fakewa da tashen suna fadan daban, sace-sace da yi wa mutane kwacen wayoyi.

“Haka kuma, sukan je teburin mai shayi, ko su samu masu abinci su dasa musu wawa,” inji Kiyawa.

Da wannan ne kakakin ’yan sandan ya yi gargadin iyaye da su ja kunnen ’ya’yansu domin kuwa duk wanda aka kama ya fito yin irin wannan tashe za’a a dauki mataki a kansa.

Mene ne asalin tashe?

Tashe a kasar Hausa wata dadaddiyar al’ada ce ta Bahaushe wacce ake danganta ta da al’adunsa masu nasaba da addini.

Irin wadannan al’adu su ne wadanda suka samo asali daga tasirin da addinin Musulunci ya yi ga rayuwar Hausawa ta yau da kullum tun bayan da addinin musuluncin ya zo kasar Hausa ta hanyar Larabawa fatake wadanda suka zo kasar Hausa tun wajajen karni na sha takwas.

Kamar yadda kalmar ta zo wato tashe, asalin wannnan wasa da samari da ‘yan mata suke aiwatarwa a cikin watan azumi ana yinsa ne da nufin tasar da masu barci su tashi su yi sahur.

Wanda kuma daga baya sai aka rinka gabatar da shi a duk lokacin da watan azumi ya kai kwana goma.

Wato da zarar an gama goma ta marmari za ka ga da yamma ko da almuru ko kuwa da dare bayan an ci abinci kuma an gabatar da sallar asham samari da ýan mata suna ta karakaina suna aiwatar da irin tashen da suka shirya.

Haka kuma wasan tashe wasan kwaikwayo ne da matasa suke aiwatarwa don su fadakar kuma su nishadantar da masu ibada wadanda suka sha yunwa da kishirwa kuma suke bukatar hutu da raha.

Wani babban makassudin yin tashe shi ne yadda yake koyar da darussa da dama a kowane fanni na rayuwa.

Ta yadda masu gabatar da tashen sukan yi kokarin kwaikwayon wata dabi’a mai kyau ko marar kyau da wasu suke yi a cikin al’umma wacce ake son su gyara saboda muninta ko kuma su dore saboda kyawunta don ci gaban alúmma.

Don haka a iya cewa tashe wata makaranta ce ta koyar da tarbiyya da al’adar Hausawa.

A cikin wasannin tashe kuma har wayau akwai hannunka mai sanda ga shugabanni da magidanta da kuma malamai akan yadda suka saki hanya ko kuma yadda ya kamata su yi don shugabantar alúmmar da suke a ciki.

Masu tashe kan yi shiga da ado da kuma magana irin ta duk wanda suke son su kwaikwaya domin su samu isar da sakonsu ga al’umma.

Haka kuma masu gabatar da tashe sukan bi gida-gida ko kasuwanni da kuma sauran wurare inda mutane ke taruwa su yi masu tashen, tare da gabatar da wakokin tashe a wani sa’in ma har da kida da rawa sukan hada.

A yayin da su kuma masu kallo ko sauraron tashen ke basu kyaututtuka na kudi ko hatsi ko kuma wani abin marmari.

Tashe ya kasu kashi-kashi, misali akwai tashe na ’yan mata da kuma na samari.

Anan ana nufin yara samari sukan ware tawagar sa’annin su sai su gabatar da nasu wasan tashen ba tare da cudanyawa da ’yan mata ba, haka kuma ’yan matan su ma sukan yi nasu, sannan kuma kowannen su ya sha banaban da juna.

Wato irin wasan tashe da wakokin da ýan mata suke yi ya banbanta da na samari. Sai dai a wasannin tashe da dama da ’yan mata ke yi sukan yi shiga irin ta maza.

Wasu daga cikin wasannin tashe na samari sun hada da wasan Gwauro ya tsinke, sakan ni in ciwo dawo, mai kacaniya, ka yi rawa dan malam, dokin kara, da mace ba gaba da dai sauransu.

Daga cikin wasannin tashe na ’yan mata kuma akwai; Ga mairama ga Daudu, mai ciki, Asha ruwa, da sauransu.

Akwai kuma wasu nau’in tashe da manya ke gabatarwa da dama wadanda akasari ana yinsu ne a fada da kuma gidajen masu hannu da shuni.

Wasan tashe wasa ne wanda za a iya kirkira duba da irin kalubalen da alúmmar da ake ciki take fuskanta da yanayin faruwar wani muhimmin abu a shekarar da ake gabatar da shi.

Dukkannin masu gabatar da wasannin tashe kama daga yara da samari da manya sukan samu tarba mai kyau da kuma kyautuka daga jama’a ganin yadda al’ummar Hausawa suke sane da muhimmancin tashe ga al’ada ko rayuwar Hausawa, musamman ma ta irin darussan da ake dauka daga wasannin na tashe.

Yadda ake gabatar da wasan tashe na ‘Sakan ni in ciwo dawo’

Wasan tashe na sakanni in ciwo dawo wasa ne da samari suke gabatarwa, a inda za su zabi daya daga cikinsu sai a tube masa riga ayi masa ado a jikinsa da farar kasa sannan a shafa masa bula a fuska.

Daga nan kuma sai a samo igiya doguwa a daura masa a kwankwaso, sai wani ya rike igiyar ta bayansa.

Su kuma sauran samari suna biye shi kuma wanda aka daura ma igiyar yana gaba suna shiga gida-gida, inda da zarar sun shiga sai ya yi kokarin ya zabura yana son ya ruga ya shiga dakin da yake a cikin gidan da suka shiga yana fadin; “Sakan ni in ciwo dawo.”

Shi kuwa wanda yake a rike da igiyar yakan dage ya jawo shi baya sauran yara kuma suna bashi amsa suna fadar “dakin na gidanku ne?” haka dai zai dinga yi shi kuma wanda yake a rike da shi yana komowa da shi baya.

Darasi

Darasin da wannan wasan tashe yake koya ma yara shi ne yaro zai san cewa taba kayan da ba nashi ba laifine babba a cikin alúmmar Hausawa.

Ta yadda ana nuna ma yara cewa ko da ma ace gidan danginka ne ko na wani na kusa da kai to ba ma wani abu da yake da muhimmanci ba ko da dawo ne wato fura wacce ka ke zaton kafi karfinta a wannan gida bai kamata ka yi gaban kanka ka sanya hannu ka dauka ba tare da masu gidan sun baka ba.