✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Shin da gaske ne Dangote na fama da karayar arziki?

Ga gaskiyar abin da bincikenmu ya gano

A ’yan kwanakin nan, labari ya karade kafafen yada labarai a Najeriya cewa hamshakin attajiran nan na nahiyar Afirka, Aliko Dangote, na fama da karayar arziki.

Lamarin dai a cewar rahotannin, ya kai ga dan kasuwar na neman tallafi domin ya samu ya karasa aikin gina matatar mai da yake a Jihar Legas.

Sai dai, binciken Aminiya ya gano cewa bisa la’akari da hada-hada da kuma samun rukunin kamfanonin Dangote, hakan ya sa labarin karayar arzikin Dangoten ya zama ba gaskiya ba.

Domin kuwa, masanin hada-hadar kudi kuma mawallafin jaridar Money Central, Patrick Atunya, na da ra’ayin cewa rashin sanin hada-hadar kudade ya sanya wasu ke ganin Dangoten ya karye.

Sabanin yadda wasu ke kallon lamarin, masanin ya ce Kamfanin Sarrafa Simintin Dangote kadai na taka muhimmiyar rawa game da arzikin attajirin saboda karfin da yake da shi a gida da waje.

Ya ce a 2021 kadai, gudunmawar da kamfanin simitin ke bayarwa ga sauran kamfanonin Dangoten, ya haura kashi 90 cikin 100.

Sannan kudin shigar da kamfanin ya samu a 2021, ya karu zuwa kashi 34 cikin 100 wanda ya kai Naira tiriliyan N1.383, sannan biliyan 346.4 bayan an cire haraji da sauransu.

A hannu guda, hasashen ‘Fitch Ratings’ ya nuna kamfanin simitin zai rika samun riba ta akalla biliyan $1.1 duk shekara tsakanin 2022 da 2025, wanda hakan zai sanya kamfanin zama daya daga cikin kamfanonin simitin da ke kan gaba a fadin duniya.

Ita kuwa cibiyar tantance karfin arziki ta Amurka, cewa ta yi Aliko Dangote na da bukatar zunzurutun kudi biliyan Dalar Amurka biliyan 1.1, kwatankwacin Naira biliyan 900 domin kammala aikin kafa matatar mansa da ke Legas.

A cewar Atunya, idan aka takaita a kan ciniki da kuma kudaden da kamfanin simitin Dangote kadai ke samu, lamarin ya wuci gaban a ce attajirin na fama da karayar arziki.

Sannan yana da tarin kadarorin da za su kare shi daga afkawa cikin rukukin karayar arziki.

Da alama dai an ba da himma wajen yada labarin karayar arzikin Dangoten ne duba da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na da yakinin bayan kammalawa, matatar man za ta taimaka gaya wajen ci gaban kasa.

Ko a watan Afrilun da ya gabata, an ji Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana matatar  a matsayin wadda za ta samar da sauyi mai ma’ana ga ci gaban Najeriya, da ya hada da kawo karshen shigo da mai daga ketare, samar da aiki ga ’yan kasa da sauransu.