More Podcasts
Gaskiya da rikon amana suna cikin dalilan da suka sa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi fice a siyasar Arewacin Najeriya.
Wasu masana da ma makusantar tsohon shugaban ƙasar dai suna ganin Arewa ta yi rashi kuma zai yi wuya a samu makwafinsa.
Yayin da ake binne marigayin, hankalin wasu ’yan Najeriya ya fara komawa kan yiwuwar samun wanda zai iya maye gurbinsa a fagen siyasar Najeriya.
- NAJERIYA A YAU: Abin Koyi Daga Rayuwar Buhari —Makusantansa
- DAGA LARABA: Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan