✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: An binne gawar Buhari a Daura

Buhari ya rasu shekaranjiya Lahadi a wani Asibiti da ke birnin Landan.

An kammala yi wa tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari sallar jana’iza tare da sanya shi a makwancinsa na ƙarshe a yammacin wannan Talatar.

An gudanar da sallar jana’izar ce bayan Sallar La’asar a wani fili da ke kusa da gidan marigayin da ke Daura na Jihar Katsina.

Wannan na zuwa ne bayan gawar marigayi tsohon shugaban ƙasar ta isa mahaifarsa Daura wadda aka ɗauko daga filin jirgin saman Katsina bayan isowarta daga Landan.

Gawar ta samu rakiyar Shugaba Bola Tinubu, da mataimakinsa Kashim Shettima, da uwargidan marigayin, Aisha Buhari da kuma wasu daga cikin iyalansa.

Daga cikin waɗanda suka sallaci gawar tare da Tinubu da akwai shugabannin ƙasashen duniya irin su na Gambia, Adama Barrow da na Chadi, Mahamat Déby da na Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embaló, sai kuma tawagar gwamnatin sojin na Jamhuriyar Nijar a ƙarƙashin jagorancin Firaministan ƙasar Ali Lamine Zeine da wasu ministoci da malaman addini.

Haka kuma, tsohon shugaban Jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou shi ma ya samu halartar jan’izar.

Aminiya ta ruwaito cewa an bai wa iyalai da ’yan uwan mamacin damar yin bankwana da shi gabanin sallar janazar, inda suka taru a jikin motar ɗaukar gawar suna kuka tare da yi masa addu’a.

Yadda jama’a suka yi cikar ƙwari a gaban kabarin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari

Ga wasu hotunan bayan kammala rufe tsohon shugaban ƙasar a kabari