✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin da gaske Messi zai koma Barcelona?

Mahaifin Messi ya gana da Joan Laporta kan komawarsa Barcelona.

Lokacin da Messi ya bar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, manazarta tamaula sun bayar da tabbacin cewa akwai yiwuwar dan wasan ya sake komawa kungiyar wata rana.

Sai dai an fi tsammanin dan wasan ya koma kungiyar a matsayin mai fada a ji, ba a matsayin dan wasa ba.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa mahaifin Mess, jorge Messi wanda shi ne wakilinsa ya gana da shugaban Barcelona Joan Laporta kan yiwuwar komawar dan wasan Barcelona.

Dan wasan bai koma PSG da kafar dama saboda har yanzu ya gaza tabuka abun kirki, wanda kuma ko a karshen mako sai da magoya bayan PSG suka yi wa dan wasan ihu kan rashin kokari da suka yi wajen gaza cire Real Madrid a gasar Zakarun Turai.

Kazalika, komawa Barcelona ga Messi a matsayin dan wasa ba abu ne mai sauki ga dan wasan ba, duba da irin abin da ya faru da Neymar shekara uku da suka gabata da ya nuna sha’awar komawa kungiyar.

Messi ya rattaba wa PSG yarjejeniyar shekara biyu, inda zai buga mata kwallo har zuwa karshen kakar wasanni ta 2022/2023.

Haka zalika, ba lallai kocin Barcelona, Xavi ya bukaci Messi a kungiyar ba duk da cewa abokai ne a baya, la’akari da shekaru sun cimma Messi.

A halin yanzu Barcelona ta mayar da hankali ne wajen gina ginshikinta da matasan ‘yan wasa a kungiyar da za ta ci moriya su a gaba.

Magoya bayan Barcelona za su so Sarkinsu ya sake dawowa kungiyar, sai dai abu ne mai wuya ga shugabannin kungiyar su aminta duba da shekarunsa da kuma albashin da ya ke dauka.

Kari a kan haka, kungiyar na cikin matsin tattalin arziki wanda shi ne dalilin da ya sa tun farko ta raba gari da dan wasan.