✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin da gaske baraka ta kunno kai tsakanin Buhari da Tinubu?

Ba abin mamaki ba ne in mutane sun tsinkayi Tinubu lokacin da Buhari ya yi magana a kan Legas

A ranar Alhamis, Kakakin Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ya fitar da wata sanarwar kan gutsiri-tsoman da ake ta yi kan tsamin dangantaka tsakanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kuma jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A yayin wata tattaunawarsa da Gidan Talabijin na Arise News, Shugaba Buhari ya yi tsokaci kan batutuwa da dama, amma kalamansa kan batun karba-karba a jam’iyyar APC ya fi daukar hankulan jama’a.

“Ba zai yiwu ka zauna a Legas alal misali ka yanke makomar APC kan tsarin karba-karba ba,” inji Buhari, lokacin da yake amsa wata tambaya yayin tattaunawar.

Akwai wasu alamu da ke nuni da cewa Tinubu na da sha’awar ganin ya gaji Buhari a matsayin Shugaban Kasa.

Ko da yake tsohon Gwamnan na Legas bai fito ya bayyana hakan ba karara, amma wasu da ake ganin yaransa ne sun yi ta karade sassa daban-daban na kasar nan suna nema masa goyon baya.

Kazalika, ’yan bangarensa na kan gaba wajen kira da a mayar da akalar mulki zuwa Kudancin Najeriya a shekarar 2023.

Buhari ya yi wankin babban bargo

A yayin tattaunawar dai da Gidan Talabijin din na Arise, Buhari ya kuma ce, “Babban burin wannan gwamnatin bai wuce ganin APC ta dore a kan mulki ba. Saboda haka kamata ya yi mu kyale jam’iyyar ta yi abinda ya dace.

“An fara sauya fasalin jam’iyyar tun daga tushe har zuwa sama ta hanyar sabunta rijistar ’yan jam’iyya. Kowanne dan jam’iyya yana da ruwa da tsaki a ciki.

“Nan ba da jimawa ba za mu yi babban taron jam’iyyar, kuma babu wani mamba da za a bari ya yi mata karan-tsaye, su suke da wuka da nama. Babu wani wanda zai zauna a Legas ya tsara yadda abubuwa za su wakana.”

Sai dai ambaton Legas da Shugaban ya yi karara ya tayar da kura, domin hatta masu karancin ilimin siyasa sun san cewa babban jigon jam’iyyar a jihar ba wai Gwamnan Jihar, Babajide Sanwo-Olu ba ne, Tinubu ne.

Hukuncin Tinubu akalla a Jihar ta Legas tamkar yankan wuka ne. A Najeriya kuma gaba daya, shine dan siyasa mafi karfin fada-a-ji, a jerin takwarorinsa da suka rike mukamin Gwamna tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007.

Ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa ’yan siyasa da dama har suka zama wasu. Tun bayan barinsa Gwamnan Jihar da ke zama cibiyar kasuwancin Najeriya, yana ci gaba da taka rawar gani wajen juya akalarta.

Saboda haka, ba abin mamaki ba ne in mutane sun tsinkayi Tinubu lokacin da Buhari ya yi magana a kan Legas a siyasar kasa, musamman abin da ya shafi jam’iyya mai mulki.

Idan ma mun ce alal misali, Buhari ba shi da wata nifaka kan Tinubu a wadancan kalaman nasa kamar yadda Garba Shehu ya yi ikirari, rashin ganin fuskar Tinubun yayin ziyarar aikin da Buhari ya kai Legas ta kwana daya, ta jefa alamomin tambaya a zukatan mutane da dama.

Batan-dabon Tinubu yayin ziyarar Buhari a Legas

Yayin ziyarar ta makon jiya dai, shugaba Buhari ya kaddamar da wasu ayyuka da Gwamnatin Tarayya da ma ta jihar suka aiwatar. Daga cikinsu akwai aikin titin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan a Ebute Metta, aikin samar da tsaro kan hanyoyin ruwan Najeriya da ake kira da Deep Blue Project a Apapa da dai sauransu.

Wadannan muhimman ayyuka ne da suka sami halartar Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, Gwamnoni da Ministocin yankin Kudu maso Yamma, sarakunan gargajiya da dai sauransu.

Wannan dai ita ce ziyarar farko da Buhari ya kai Legas tun bayan da Babajide ya zama Gwamnan Jihar, amma ba a ga ko keyar Tinubun ba.

Tsawon lokaci dai su duka biyun ke nesa-nesa da juna, ko da yake a ’yan kwanakin baya sun hadu a Fadar Shugaban Kasa bayan rasuwar Babban Hafsan Sojin Kasa, Janar Ibrahim Attahiru.

Hakan dai na nuni da yuwuwar barakar da ke tsakanin mutanen da suka yi wa jam’iyyar PDP rubdugu, har ta kai da a karon farko an kayar da jam’iyya mai ci a Najeriya a 2015, lamarin da ya kawo karshen shekaru 16 na mulkinta.

Yayin waccan ziyarar dai ta Tinubu a Fadar ta Shugaban Kasa, an ga su biyun suna gaisawa kuma sun dauki hoto tare. Shin amma hakan ya isa ya nuna cewa babu tsamin dangantaka a tsakaninsu?

Koma dai menene, wani abu da yake a bayyane shine nan ba da jimawa ba za a fara siyasar 2023 kuma akwai abubuwan kallo da yawa a cikinta.