✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin an sauke Buni daga Shugabancin APC?

Gwamnan Neja ya shiga taron sirri da wasu kusoshin jam'iyyar a hedikwatarta

An shiga rudu game da gaskiyar sauke Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, daga matsayinsa na Shugaban Rikon Jam’iyyar APC, tare da maye gurbinsa da Gwamna Abubakar Sani Bello na Jihar Neja.

A safiyar Litinin ne dai Gwamnan Jihar Nejan ya bayyana a hedikwatar jam’iyyar ta kasa da rakiyar wasu kusoshin jam’iyyar, inda zuwansu ke da wuya suka fara ganawar sirri.

Shaidu sun ce Gwamna Bello ya ajiye motarsa ne a wurin da aka kebe wa shugaban jam’iyyar, wanda a halin yanzu yake kasar Jamus, domin duba lafiyarsa.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da ke nuna an sauke Buni ko Gwamna Bello ya maye gurbinsa a matsayin shugaban rikon jam’iyyar APC na kasa.

Jita-jitar sauke Buni

A ranar Litinin ne aka wayi gari jami’an tsaro sun mamaye Hedikwatar APC ta Kasa da ke Abuja, a yayin da wasu rahotanni ke cewa Shugaba Buhari ne ya ba da umarnin sauke Buni da kuma maye gurbinsa.

Kafar yada labarai ta Prime Business ta ambato wasu majiyoji daga Fadar Shugaban Kasa na cewa kafin Buhari ya kama hanyarsa ta zuwa Landan domin ganin likita a ranar Lahadi ya ba da umarnin cewa Bello ya karbe ragamar shugabancin jam’iyyar.

Ba gaskiya ba ne —Yekini Nabena

Amma a safiyar Litinin Kwamitin Rikon APC da Buni ke jagoranta ta musanta batun saukewar da ake dangantaw da Buhari.

“Jam’iyyar APC mai bin doka ce kuma tana da dokoki, ba majiyoyi masu fakewa da sunan wani ke sanar da sauyin shugabanci ba,” inji sanawarrar da Sakataren Rikon jam’iyyar, Sanata John James Akpanudoedehe, ya fitar.

Akpanudoedehe ya bukaci ’yan jam’iyyar da sauran jama’a da su yi watsi da labarin su mara wa shugabancin Buni baya domin gudanar da babban taron jam’iyyar cikin nasara.

Majiyarmu ta ce bisa dukkan alamu, ya zuwa lokacin kwamitin rikon da Buni ke jagoranta na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da baban taron jam’iyyar da ke kara matsowa.

A safiyar Litinin din ne dai aka girke jami’an tsaro dauke da makamai a hedikwatar jam’iyyar da ke unguwar Wuse 2 a Abuja domin tabbatar da bin doka da oda.

Isowar Gwamna Bello

Sai dai kuma jim kadan bayan nan, sai ga Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya iso wurin, inda ake ganin ya je ne domin maye gurbin Buni, wanda ya tafi duba lafiyarsa a kasar Jamus.

Wasu majiyoyi na cewa ana sa ran Bello zai rantsar da shugabannin jam’iyyar na jihohi 36, a wani taron sirri da za a gudanar a ranar Litinin din.

‘Bello na da wata manufa’

A halin da ake ce, Mataimakin Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar APC na Kasa, Yekini Nabena, ya soki kiran da Bello ya yi na gudanar da taron gaggawa na Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar (NEC).

Nabena ya ce akwai lauje cikin na a kiran taron, wanda ya ce na da alaka da cimma manufar Gwamna Bello na zama dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa a zaben 2023.

A cewarsa, Gwamna Bello ba shi da hurumin kiran taron, domin ba gwamnan ba ne Shugaba ko Sakataren Kwamitin Rikon Jam’iyyar ta Kasa, shi mamba ne kawai.