A ranar Litinin da ta wuce ne wato 3 ga watan Oktoban nan Musulmin duniya suka yi maraba da shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1438 Bayan Hijira. Ranar ce ta kasance 1 ga watan Muharram. Musulmi kan gane shigar sabon wata ne idan watan da ya gabace shi ya cika kwanaki 29 ko 30, dalilin da ya sa Kalandar Musulunci ta kunshi kwanaki 354 ko 355 a shekara.
An fara amfani da kirgen watanni 12 na kalandar Musulunci ne a zamanin Khalifan Manzon Allah na biyu Umar dan Khaddab a shekara ta 16 Bayan Hijira shekata 637 Miladiyya.
Watan farko na kidayar watannin Musulunci wato Muharram da aka fi sani da watan tunatarwa yana daga cikin watanni hudu da suka fi daraja a Kalandar Musulunci. Muharram yana nufin “hani” kuma Musulmi da dama suna azumi a cikinsa da neman kaurace wa daga abubuwa marasa kyau.
Duk da dai ba a dauki watan a mtsayin na shagulgula kamar ranakun Idin Layya da Idin karamar Sallah ba, amma ana girmama shi ganin yadda Manzon Tsira Annabi Muhammad (SAW) ya kafa Daular Musulunci a cikinsa a garin da ake kira a baya da Yathrib wato garin Madina a cikin watan Muharram. Manzon Allah (SAW) ya yi kaura daga Makka zuwa Madina ne a shekarar 622 Miladiyya, abin da ake kira Hijira, wanda shi ne ginshikin farko na kalandar Musulunci. Wannan ne ya nuna Musulmi sun zama al’umma mai zaman kanta da tsarin kalandarta.
Musulmi kan yi azumin nafila a watan Muharram na Tasu’a da Ashura duk da dai ba farilla ba ne. Watan Muharram yana daga cikin watanni hudu da aka hana yin yaki a cikinsu. Sai dai akwai bambancin fahimta game da watan Muharram a tsakanin ’yan Shi’a da kuma ’yan Sunni. Masu bin akidar Shi’a kan yi amfani da ranar 10 ga watan Muharram ne a matsayin daya daga cikin ranakun makokin rashin marigayi Imam Hussaini bn Ali, a Karbala wato jikan Manzon Allah (SAW) da surukinsa Sayyidina Ali ya haifa. Kuma ana kiran ranar 10 ga watan da Ranar Ashura. Su kuwa Musulmin da ke bin akidar Sunni sun dauki ranar 10 ga watan Muharram ce a matsayin ranar da suke tuna yadda Annabi Nuhu (AS) ya kera kwalekwalen da ya tserar da al’ummarsa da kuma ranar da Allah Ya tserar da Musa daga zaluncin Fir’auna. Ga mafi yawan Musulmi suna amfani da ranar 1 ga watan Muharram a matsayin ranar da suke auna kai ta hanyar yin ibada da neman gafarar Ubangiji da kaskantar da kai da karanta Alkur’ani a asirce ba tare da yin wata hayaniya ba ta hanyar tunawa da abubuwa marasa kyau da suka yi a shekarar da ta wuce da kuma irin shirin da suke yi a kan sabuwar shekara.
Ya kamata Musulmin duniya su dauki shigowar shekarar 1438 a matsayin wacce za ta tuno musu da irin sadaukarwar da Musulmin farko suka yi, domin su ma su ci gaba da kare martabar addininsu. Amfani da Kalandar Musulunci ibada ne kuma wata muhimmiyar manuniya ce da ke nuna manyan abubuwan da suka faru a tarihi da za su taimaki Musulmi wajen sanin tushensu tare da fadada iliminsu game da addinin da kuma tarihi. Farkon kalandar Musulunci har wa yau wata manuniya ce na nuna tarihin Musulunci da yadda za a a nazarci juyin juya-hali da cikakken sauyin da ya kawo wa al’umma ta hanyar cikakkiyar ’yan uwantaka. Lamarin bai takaita ga kara imanin mutum kadai ba, har ma da kasancewar Musulunci a matsayin addini na rayuwa. Kuma da dama daga cikin ayyukan ibada da suka hada da Zakka da Azumi da aikin Hajji suna ginuwa ne kan wannan kalanda. Kuma lokaci da za a waiwayi shekarar da ta gabata don shirya wa wadda za a shiga tare da niyyar kara kusantar Allah da AnnabinSa ta hanyar ayyukan ibada kuma a tabbatar da adalci da zaman lafiya. Ya dace Musulmi su kyautata dangantakarsu da Allah wajen yin ayyukan ibada tare da wanzar da adalci da zaman lafiya. Wajibi ne su tuba su zama nagari ta hanya yin ayyukan kwarai da yin karatun Alkur’ani da bayar da sadaka da kula da iyali da neman ilimi da taimaka wa mabukata da yin godiya ga Allah (SWT) kan irin ni’imar da Ya yi wa bayinSa.
Muna yi wa daukacin al’ummar Musulmi murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1438 kamar yadda muke fata Musulmi za su yi amfani da wannan dama wajen samar da zaman lafiya da cigaba da hakan zai kawo karshen matsalar tarbarbarewar tattalin arzikin da duniya ta tsinci kanta a ciki.
Shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1438 BH
A ranar Litinin da ta wuce ne wato 3 ga watan Oktoban nan Musulmin duniya suka yi maraba da shigowar sabuwar shekarar Musulunci ta 1438…