Shugaban wani bangare na Boko Haram, Abubakar Shekau ya bar dajin Sambisa kafin sojoji su kai hari inda suka samu nasarar mamaye yankin da yake zaune.
Aminiya ta samu rahoton cewa yanzu haka Shekau ya koma yankin wasu kauyuka ne a Karamar Hukumar Kunduga, kamar yadda wasu maharba suka shaida wa Aminiya.
Sun shaida wa Aminiya cewa daruruwan ‘yan Boko Haram din tare da wasu wadanda suka yi garkuwa da su ciki har da sauran ‘yan matan Chibok sun mamaye yankin Gambale.
Sun kara da cewa Shekau yana nan a tsakanin kauyukan Dumur da Duhuwa, sannan kuma sauran mayakansa suna tsakanin Faltruram da Darfada da Uye da Barkin da Lukshe da Luksheab-amarwa da Mulgwaulawanti da Gwarimari.