✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shekarau ya koma PDP

Ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanatan Kano ta Tsakiya, Ibrahim Shekarau, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa PDP a hukumance.

Shekarau ya bayyana hakan ne ranar Litinin a gidansa da ke unguwar Mundubawa da ke Kano.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar ta PDP, Atiku Abubakar da Shugaban jam’iyyar, Sanata Iyorchia Ayu na daga cikin jiga-jigan da suka halarci bikin komawar.

Kazalika, Shekarau ya rubuta wasika ga Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) yana sanar da janyewarsa daga takarar Sanata a karkashin jam’iyyar NNPP.

Sauran jiga-jigan jam’iyyar da suka halarci taron sun hada da Mataimakin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar kuma Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa da Gwamnonin Sakkwato da na Taraba, Aminu Tambuwal da Darius Ishaku.

Ragowar sun hada da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Namadi Sambo, Shugaban Kwamitin Amintattu na jam’iyyar da tsoffin Gwamnonin Jigawa (Sule Lamido da Saminu Turaki) da na Sakkwato (Attahiru Bafarawa) da na Kaduna (Ahmed Makarfi) da na Adamawa (Boni Haruna) da sauransu.