✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 36 da fara wasan kokawa a Nijar: Jihar Dosso ta lashe gasar takobi ta bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka kammala wasan kokowar gargajiya da aka saba yi a duk shekara a Nijar. Kokowa dai a kasar…

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka kammala wasan kokowar gargajiya da aka saba yi a duk shekara a Nijar. Kokowa dai a kasar na daya daga cikin wasannin gargajiya da ‘yan kasar ke alfahari da shi. Gasar ta bana an yi ta ne a Jihar Agades kuma a garin na Agades wanda sauran jihohin kasar suka turo da ‘yan wasansu kamar yadda tsarin wasan yake,inda kowace jiha ke turo da akalla ‘yan wasa goma wadanda ke karawa a tsakaninsu a inda a karshe ake fitar da mutane hudu wadanda kuma daga cikinsu ne ake fitar da zakara. Sai na biyu da na uku da na hudu wadanda ake musu kyaututtuka iri daban-daban. Ana dai cin takobi ne a wajen wannan gasa.

Gasar ta bana Jihar Dosso ce ta ci wannan takobi ta hanyar dan kokuwarta mai suna Issaka Issaka wanda ya yi nasara ga abokin karawarsa mai suna Sabo Abdouley na Jahar Yamai wadda ita ce ke rike da wannan takobi a cikin mintuna biyu da fara wasan. Ita dai Jihar Yamai wadda kuma ita ce babban birnin kasar ta Nijar, ta ci wannan takobi ne a bara a wasan da aka yi a Jahar Diffa. Bisa ga al’ada, ana zagaya wannan wasa ne a tsakanin jihohin kasar a duk shekara. Ita dai Jahar ta Dosso wannan shine karo na farko da ta ci wannan Takobi a cikin shekaru 36, domin rabonta da cin wannan takobi tun cikin shekara ta 1979 bayan wani dan kokuwarta mai suna Salma dan Rani ya ci takobin, sai kuma a wannan karo da Issaka ya sske kawo takobin a Jahar ta Dosso.
‘Yan Kokowar hudu da suka rage kuma suka fafata a wannan rana ta karshe su ne: Adamu Abdu da Sabo Abdouley daga Jahar Yamai,sai Salai Dauda daga Jiha mai masaukin baki wato Agades tare da shi Issaka Issaka daga Jahar Dosso wanda kuma shi ya zamo zakara yayin da abokin karawarsa Sabo Abdouley ya zamo na biyu. Salai Dauda na Agades ne ya zamo na uku, shi kuma Adamu Abdu daga Yamai ya zo na hudu.
Jihohin da suka halarci wannan wasan kokuwar na Agades sun hada da ita kanta Agades sai Dosso da Diffa da Maradi da Tahoua da Tillabery da Yamai da kuma Zinder.