Fitaccen Malami kuma Limamin Juma’a a garin Gusau na Jihar Zamfara, Sheikh Sa’id Maikwano ya caccaki Sheikh Aminu Daurawa kan abin da ya faru tsakaninsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf dangane da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano.
Sheikh Maikwano ya soki yadda Daurawa ya lashe amansa kan ajiye aikin Hukumar Hisbar bisa wasu kalamai da gwamnan ya yi wanda Malamin ya ce sun rage masa kwarin gwiwa.
- A bai wa mata jagorancin Nijeriya saboda maza sun gaza — PDP
- Muna Fargabar Za A Samu Hare-Hare A Wuraren Tarukan Jama’a — DSS
Sheikh Maikwano a cikin wani faifan bidiyo wanda ya karade shafukan sada zumunta musamman Facebook ya ce abin da Daurawa ya yi raini ga gwamnati kuma sam bai kamata ba.
Malamin ya ce yunkurin da Daurawa ya yi, da kuma kalaman da fadi maganganu ne na raini wanda ba su kamata ba.
“Sheikh Daurawa ya shahara ne ta dalilin gwamnati ba ta dalilin karatu ba. Ya kamata a ce ya kare mutuncin gwamnati ba kuma ya zage ta ba,” a cewar malamin.
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi sulhu da Sheikh Daurawa bayan murabus din da malamin ya yi daga shugabancin hukumar.
Tuni dai Sheikh Daurawa ya koma bakin aiki bayan an shawo kansa a wani taron sirri da Zauren Malaman Kano ya jagoranta a Fadar Gwamnatin Kano.