✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sheikh Dahiru Bauchi ya bukaci mabiyansa zu zabi Atiku

Ya bayyana hakan ne a wani sakon murya ranar Alhamis

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, kuma daya daga cikin jagororin darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bukaci mabiyansa su zabi dan takarar Shugaban na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a zaben ranar Asabar.

Malamin ya bayyana hakan ne a wani sakon murya da ya fitar ga mabiyansa ranar Alhamis.

Kalaman nasa na zuwa ne yayin da ya rage kwana biyu kafin zaben Shugaban Kasar.

A cewarsa, “Allah Ya kawo mu lokacin zabe, jama’a ’yan uwana ’yan Najeriya. Annabi (S.A.W) na cewa bai kamata a ciji mumini sau biyu a rami daya ba.

“Na ji wasu mutane na cewa a zabi wanda zai dora a kan inda aka tsaya. To ai inda muka tsayan ba dadi muka ji ba, balle mu dora a kai. Mutum sai ya ji dadi yake cewa a kara min.

“Saboda haka ina kira da zabi inda za a sami sauki, ko Allah zai canza mana.

“Mutanena sun ba da shawara Atiku za su zaba, ni kuma tun da ga inda suka dosa ba zan rabu da su ba. Zan tsaya tare da su mu ga abin da Allah zai yi. Allah ya zaba mana abin da zai zama alheri,” in ji malamin.