✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Shehu Giant: Shugaban PDP na Kaduna ta Tsakiya ya rasu

A safiyar Talata ce Allah Ya yi wa Shehu Giant, tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa ne, cikawa a Asibitin Sojoji na 44 da…

Shugaban Jam’iyyar PDP Reshen Kaduna ta Tsakiya, Shehu Ahmad Giant, ya riga mu Gidan gaskiya.

A safiyar Talata ce Allah Ya yi wa Shehu Giant, wanda tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa ne, cikawa a Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna.

Usman Muhammad Gwarzo, ya sanar ta shafinsa na Facebook cewa, “Innalillahi wa Innah ilaihi Raji’un! Yanzun nan muka samu sanarwar rasuwar Honorabul Shehu Ahmed Giant, tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, kuma Shugaban PDP na Mazabar Kaduna ta Tsakiya a yanzu.”

Sanarwar ta ce za a sallaci marigayin a Masallacin Sultan Bello da ke Unguwar Sarki Kaduna bayan Sallar Azahar.

Kafin rasuwarsa, ya jima yana fama da rashin lafiya.