Mun ga rubutunka ne game da mai tari da ciwon kirji sanadiyyar aiki cikin kura, inda ka ce ya je a duba kirjin. To wadanne shawarwari za a ba masu aiki a cikin kura domin kiyaye lafiyarsu?
Amsa: Mutane ma’aikata da ke aiki cikin kura suna cikin hadari babba na kamuwa daga wasu cututtuka da wannan wurin aiki nasu kan iya sa musu. Wadannan wuraren aiki da ke da kura kuwa sun hada da wurin kwasar yashi, wurin gini ko haka, wurin fasa dutse, wurin tonon ma’adinan cikin kasa, wurin sarrafa kayan rufi kamar kwanon rufin asbestos, da gonaki, da masu yawan shiga kurar Sahara kamar fatake ko ‘yan fasa-kwauri, da jami’ai masu damara, masu shiga filin daga, duk masu aiki a nan sune ke cikin hadarin samun matsala a huhunsu sanadiyyar kura. Kai har ma da mazauna gefen titunan da suka dade ba kwalta inda ababen hawa ke ta da kura a kullum suna cikin hadari.
Bincike ya kiyasta cewa masu aiki a cikin kura suna iya shakar kurar da ta kai kilo guda a tsawon shekarun da suka dauka suna aiki cikin kurar. Iya yawan shekarun mutum a wurin wannan aiki iya yawan kurar da kirjinsa ya shaka kenan. Sai dai wani abu mai sanyaya rai game da wannan yawan kura shi ne cewa kirjinmu na iya yin aikin fitar da fiye da rabin wannan kura a tsawon wannan zamani. Wadannan hanyoyi da hanyar numfashi da huhu kan bi su fitar da kurar sun hada da tare kurar da gashin hanci da na huhu, da sarrafa majina don makale kwayoyin kurar da tari da nade su cikin kwayoyin garkuwar jiki.
Duk da haka abin da hanyoyin numfashi bai samu ya tare ba zai iya saka illa a huhun ma’aikacin. Irin wadannan illoli sun hada da cutar asma da ta kansar huhu da ta cutar numfashi ta COPD irin ta ‘yan sigari da sauran ire-iren cutukan numfashi masu dadewa a jiki su sa huhu ya tattare ko ya motse, kamar asbestosis ta masu aiki a masana’antar rufin kwano mai asbestos.
To wadanne hanyoyi mutum zai bi ya kiyaye kansa daga shakar wannan kura? Akwai yadda masu kamfanoni za su yi su rage fitar da kura mai illa a masana’antunsu ko wuraren aiki, amma wannan ya shafi shugabannin ma’aikatun ne, da shugabannin kula da jin dadin ma’aikata, kuma sun san hanyoyin. Misali a wuraren da ya kamata a yi shara, kada a yi shara da tsintsiya ko wani abu mai ta da kura, sai dai inji ko motar shara wadda ba ta tayar da kura, kuma bayan an yayyafa ruwa.
A daidaikun ma’aikata akan ba da irin takunkumin nan na rufe hanci wanda zai tace kura sosai kafin mutum ya shaketa. To kamata ya yi duk mai irin wannan aiki ya tabbata ana samar da irin wadannan takunkumai a kullum, kuma a rika amfani da su a kullum. Wadannan suna matukar iya rage shigar kura huhu sosai da kusan kashi 90 % don haka kada a yi wasa da daurawa. Idan ma mutum ba a kamfani yake ba zaman kansa yake, haka nan dole ya sayi irin wadannan takunkumi domin amfanin yau da kullum. Sai kuma cin lafiyayyen abinci mai gina jiki da kayan marmari masu kara bitaman a jiki wadanda za su karfafa lafiyar kwayoyin garkuwar jiki su ci gaba da hadidiyar kwayoyin kura da mutum ke shaka.
Ya kamata masu aiki a kamfanoni irin wadannan su sani fa cewa duk wani ciwon kirji da asma da numoniya da ya same su kamfanin da yake aiki ne su za su dauki nauyin duka magungunan ciwon da aka samu a kirjinsa.
Wai mene ne amfanin tafarnuwa a jikin mutum?
Daga Surajo Yahaya, Zamfara
Amsa: Wannan tambaya ba ta shafi bangaren likitanci ba, bangaren ilmin magunguna ta shafa, watakila su za ka tambaya. Mu ma mukan ji ana cewa tana maganin matsalolin makogaro da hanyoyin numfashi. Sai dai duk binciken likitanci bai tabbatar da hakan ba har yanzu.
Mene ne amfanin shafa zuma da madara a fuska? Wai da gaske ne yana maganin kurajen fuska?
Daga Daga Rabi’a Abubakar Shuni
Amsa: Ai sai dai ki gwada ki gani tunda wannan ba fagen likitanci ba ne. Na dauka ma shafa shuni a kurajen za ki tambaya ko shi ma yana aiki.
Me ke sa kuraje a cikin baki masu zafi, amma ba sa jini kuma ba sa ruwa?
Daga Zubairu Abuja Kwatas, Gumel
Amsa: Yawanci rashin cin isassun bitaman ne ke kawo miki ko kurji cikin baki. Da za ka jera sati kullum sai ka ci wani nau’i na ganye ko na ‘ya’yan itatuwa da ka ga abin mamaki.
Wai ko bacin ciki (gudawa) cuta ce? Ni duk abin da na ci sai cikina ya baci. Ga kumburi ga ciwo.
Daga Amina M. Malumfashi
Amsa: E, duk wata gudawa bayan cin abinci cuta ce. Sai dai akwai cutuka iri biyu masu sa haka; akwai shigar kwayoyin cuta cikin, akwai kuma borin ciki. Wato borin ciki ko hanji shi ma kan sa gudawa da kumburi da ciwon ciki kamar na shigar kwayoyin cuta. Bambancinsu shi ne sai mutum ya ci wani nau’i na abinci da hanjinsa ba ya so yake samun borin ciki, misali madara, kifi, kwai, ko ayaba. Akwai wadanda in dai za su ci daya daga cikin wadannan nau’ukan abinci sai sun yini sun kwana suna gudawa. Amma dai akwai magani, wanda sai kin je asibiti likita ya tantance ko haka ne, ko kuma gudawar kwayoyin cuta ce, kafin a rubuta miki. A mafi yawan lokuta kuma daina cin abin da ke sa borin cikin ne kawai mafita, idan mutum ya gano ko mene ne.
Ni ina yawan fitsari da yawan shan ruwa sosai. Ko hakan na da alaka da wani ciwo?
Daga Muhammad Abubakar Rabo
Amsa: E, kuma a’a. Idan kana yawan shan ruwan da jikinka ba ya bukata za ka rika fitsarar da shi. To amma a wani kaulin kuma na likitoci alamun ciwon suga haka yake farawa, yawan fitsari da yawan kishin ruwa. Don haka baka ga ta zama ba, domin yana da kyau ka je a dan maka bincike. Ba a fatan ciwo amma in kana so a tabbatar ba matsala ba ce sai ka yi aune-aune.