Suanan Littafi: SECURITY AND JUSTICE: The Patheway for Peace and
Reconciliation in Nigeria (TSARO DA SHARI’A: Tabbatattun Hanyoyin
Samar Da Maslaha Da Zaman Lafiya A Najeriya).
Marubuci: Ibrahim K. Idris
Shekarar Wallafa: 2018
Kamfanin Wallafa: Toprint Global Serbices Ltd.
Yawan Shafuka: 293
Farashi: Ba a fada ba.
Masu iya magana sun ce zaman lafiya ya fi zama dan sarki, wasu suka ce ya fi sarkin ma kansa. Kuma iyaka gaskiyar ke nan, domin kuwa babu wata harka a rayuwar duniyar nan da za ta samu ci gaba ko ta samu nasara ba tare da zaman lafiya ba. Najeriya, a matsayinta na babbar kasar bakar fata a duniya, mai dauke da al’umma sama da miliyan 180, mai dauke da mabambantan kabilu sama da 300, mai dauke da mabiya addinai daban-daban, babu shakka tana bukatar zaman lafiya, musamman ma a wannan lokaci da take fuskantar babban kalubalen rikice-rikice daban-daban, da suka hada da ta’addancin Boko Haram, fadace-fadace masu nasaba da kabilanci da na addini. Don haka, samar da wannan littafi da muke wa sharhi a yau, babbar gudunmowa ce wajen lalubo bakin zaren yadda za a samar da ingantaccen tsaro da zaman lafiya a Najeriya.
Wannan littafi, wanda kwararren masanin shari’a kuma masanin harkokin tsaro kuma uwa-uwa Sufeto-Janar na ’yan Sandan Najeriya, Ibrahim K. Idris NPM, mni ya rubuta, baya ga shafukan godiya da gabatarwa, yana dauke da babi-babi 18, wadanda a cikinsu ya tattauna muhimman tubala da ginshikan da ake bukata domin samar da dawwamammen zaman lafiya a kasa.
Babi na daya ya faro ne daga shafi na 01-18, inda marubucin ya samar gamsasshen bayani game da SHARI’A. Ya bayyana ma’anar shari’a da muhimmancinta da hanyoyin gudanar da ita da yadda za a ci gajiyar shari’a wajen hana zalunci da tabbatar da gaskiya, wadanda ta haka ne za a samar da ingantacce kuma tabbataccen zaman lafiya a cikin al’ummar kasa. “Shari’a a budaddar ma’ana, tana nufin adalci. Shari’a ba tana nufin lallai dole ne a magance kowace rashin jituwa ko rigima “daidai” ba tare da wani kuskure ba, amma tana nufin bin hanyoyin da suka dace wajen warware matsala cikin kyautatawa da adalci, inda daga karshe za ta samar da gamsasshen sakamako.” (shafi na 01).
Babi na biyu ya faro ne daga shafi na 19 ya karkare a shafi na 25 kuma marubucin ya yi bayani dalla-dalla dangane da abin da ake nufi da TSARO. Haka kuma ya yi bayani game da sulhu ko sasanci da hanyoyin da suka kamata a bi a yi sulhu tsakanin al’ummomin da suka samu matsala ko rashin jituwa. Haka kuma ya bijirar da bayanaii game da muhimmanci da ke tattare da sulhu da tasirinsa wajen samar da zaman lafiya a kasa.
“Domin samar da zaman lafiya, hadin kai, ’yancin kungiyanci, ’yancin fadin albarkacin baki da kuma ’yancin walwala, mutum na bukatar tsaro. Sai dai kuma wadannan ’yance-’yance za su kasance masu tasiri ne idan kai ma ba za ka dakile wa wasu irin wadannan ’yanci na bayyana albarkacin bakinsu ba.” (shafi na 19).
A babi na uku kuwa, marubucin ya yi kokarin bayyana tunaninsa da shawarwarinsa game da hanyoyin da suka kamata a bi wajen samar da adalci a shari’a da kuma yadda za a samar da sasanci ko sulhu tsakanin al’ummar kasa. Ya zayyana wasu matsaloli da yake ganin su ne ke yi wa harkokin shari’a kandagarki a Najeriya, musamman ma yadda harkar shari’a da gudanar da ita ke da dan karen tsada a kasar nan da kuma wasu tsare-tsaren da ke danfare a kundin tsarin mulkin kasa da sauransu.
A babi na hudu kuwa, marubucin ya tattauna wasu muhimman al’amura ne da suke zama sanadin samar da rikice-rikice a kasa, wadanda suka hada da rigingimun siyasa, fadace-fadacen kabilanci da kuma na addini. Marubucin bai yi kasa a gwiwa ba, har sai da ya kawo misalan wasu sanannun tashe-tashen hankali ko rigingimu da suka taba faruwa a Najeriya a matsayin misali. Haka kuma ya yi gargadi ga musamman ’yan siyasa da shugabannin addinai da masu rike da shugabancin gargajiya da ma sauran al’umma da su guji tayar da hankali ga al’umma domin biyan bukatun kashin kansu. Kamar yadda ya ce: “Ya kamata a yau ku san cewa tarihi zai tuna da ku ne dangane da abin da kuka gina na alheri, a yayin da kuma zai farauce ku har abada dangane da abin da kuka lalata.” (shafi na 35).
A babi na biyar, marubucin dogon tsokaci ya yi tare da nazari wajen amsa tambayar da ke cewa ‘Ko tsarin tafiyar da mulkinmu na siyasa zai magance afkuwar rikice-rikice a kasa?’ A yayin amsa wannan tambayar, marubucin ya bibiyi tarihin rikice-rikicen da suka rika faruwa a Najeriya a baya da kuma irin matakan da hukumomi suka dauka wajen dakile shi ko akasin haka. Misali, yadda rikicin Neja-Delta ke ta kwan-gaba-kwan-baya wajen faruwa. Ya bibiyi al’amuran rikicin Boko Haram da wasu daga rikice-rikicen da ke da nasaba da addini da kuma na kabilanci.
“Namijin kokarin da wannan gwamnatin take yi wajen magance tashe-tashen hankulan addini da na siyasa sun sanya an samu nasarori ya zuwa yanzu. Yanzu lokaci ya yi da ya kamata a kara kaimi wajen magance rikice-rikice a kasar nan kuma jami’an tsaro kadai ba za su iya ba. Don haka ya kamata kowa ya sanya hannu wajen tabbatar da tsaro a kasarmu.” (shafi na 49).
Babi na 6 da na 7 da na 8, daga shafi na 60 zuwa na 134, marubucin ya yi tsokaci tare da kyakkyawan bayani game da dangantakar tattalin arzikin kasa da tashe-tashen hankali a Najeriya. Ya yi bayani game da yadda za a samu nasarar mulkin dimokuradiyya a kasa irin Najeriya, inda ake samun halayyar kabilanci. Sai kuma bayanai dangane da rikice-rikicen siyasa da na kabilanci da na addini da yadda suke faruwa a Najeriya da kuma gudunmowar da mutane da kungiyoyi da jami’an tsaro ke bayarwa wajen magance su.
Wani al’amari mai matukar muhimmanci da marubucin littafin nan ya tattauna a babi na 9, shi ne batun kishin kasa da yadda za a yi zama na lumana da wanzar da zaman lafiya a kasa ta hanyar kishin kasa da samar da adalci a shari’a.
A babi na 10, 11, 12, 13, 14 da na 15, muhimman al’amura aka tattauna, wadanda za su taimaka ko suke taimakawa wajen samar da zaman lafiya da sulhu tsakanin al’ummar kasa. Akwai tsokaci game da gwamnati mai kyau, dimokuradiyya da kuma ci gaban kasa. Kafafen watsa labarai na da muhimmiyar rawar takawa a kowace kasa, don haka an yi bayanin irin rawar da za su iya takawa a yayin zabubbukan siyasa, ta yadda za a samu gudanar da zabe cikin lumana ba tare da tashin hankali ba. Sarakunan gargajiya na da matukar muhimmanci, suna da matakai da hanyoyin samar da zaman lafiya a yankunansu da al’ummarsu. Don haka, marubucin nan ya zayyana irin muhimmancinsu da irin gudunmowar da suke bayarwa wajen samar da zaman lafiya a kasa.
A babi na 16, marubucin ya yi abin nan na salon maganar Hausawa da suke cewa, wani ma ya yi rawa bare dan makada? Kasancewarsa Shugaban Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da ke kan mulki, marubucin ya yi bayanin hanyoyi da matakan da ake kan dauka, wajen samar da ingantattar Rundunar ’Yan Sanda, wacce ke aiki cikin kishin kasa da kaunar jama’a, kamar yadda ake yi a kasashen duniya da suka ci gaba.
“daya daga cikin hukumomi mafi muhimmanci a kowace kasar da ke tafiyar da mulkin dimokuradiyya ita ce Rundunar ’Yan Sanda, domin kuwa ita ce aka dora wa alhakin samar da zaman lafiya a cikin gida, kuma ita ce jakadar kawo canji ta hanyar kishin kasa.” (shafi na 234).
A babi na 17 da kuma babi na 18 kuma na karshe a littafin, marubucin ya kitse kunshiyar littafinsa da muhimman bayanan da suka danganci hanyoyin magance kowadanne irin laifuffuka a kasa, sannan kuma ya yi bayani a mahangarsa dangane da wadannan batuwa na ka’idojin aikin dan sanda da kuma hikimomi da dubarun gudanar da aikin a Najeriya.
Babu shakka kunshiyar littafin nan ta samar da rumbun ilimin da ya shafi shawarwari da hanyoyin samar da zaman lafiya a Najeriya. An rubuta littafin nan bisa nazari da binciken muhimman littattafai da mujallu da jaridu da suka shafi al’amuran shari’a, tsaro da al’amuran yau da kullum. Littafi ne da ya kamata kowane dan kasa ya mallaka, musamman ma dai shugabanni, ’yan siyasa, ’yan kasuwa, malaman addinai, masu shari’a, lauyoyi, jami’an tsaro, malaman makaranta da ’yan jarida.
Game da marubucin, Ibrahim Idris Kpotun kuwa, an haife shi ne a ranar 15 ga Janairu, 1959 a garin Kutugi, Jihar Neja. Ya shiga aikin ’yan sanda a 1984 bayan ya kammala digirinsa a fannin Noma a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. Ya kuma je Jami’ar Maiduguri, inda ya samu digiri a fannin Shari’a. Kafin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi mukamin Sufete-Janar na ’Yan Sandan Najeriya a ranar 21 ga Yuni, 2016, ya yi aiki a rundunar ta ’yan sanda a wurare daban-daban a Najeriya.