✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta kori bukatar soke zaben Tinubu da Shettima

Kotun ta kori karar da Jam'iyyar APM ta shigar na neman soke halascin zaben Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima a zaben 2023.

Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Shugaban Kasa ta kori karar da Jam’iyyar APM ta shigar na neman soke halascin zaben Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima a zaben 2023.

Mai Shari’a Haruna Tsauri ya yi watsi da ikirarin APM na cewa Kashim Shettima da Tinubu ya yi a matsayin abokin takararsa, ya yi takara biyu a lokaci guda, domin kuwa a lokacin shi dan takarar Sanata ne, wanda hakan ya saba doka.

Alkalin ya ce APM ba ta da hujjar cewa takarar Tinubu da Shettima haramtacce ne, ballanta ta kafa hujja da cewa an zabi Tinubu ba tare da halastaccen mai yi masa takarar mataimaki ba.

Ya kara da cewa bisa hujjojin da APC ta gabatar, Shettima bai yi takara biyu a lokaci guda ba, domin sai da ya ajiye kujerarsa da kuma takararsa ta Sanata kafin ya karbi takarar mataimakin shugaban kasa da Tinubu ya zaba.

Wannan na cikin hukuncin da alkalin ya fara karantawa kan karar da jam’iyyu APM da kuma babbar jam’iyyar adaewa ta PDP da kuma LP da ’yan takararsu suka shigar suna kalubalantar nasarar Tinubu da Shettima a zaben.

Hakan na zuwa ne bayan watanni da shigar da karar, wanda ’yan Najeriya da bangarorin da ke shari’ar suka jima suna jiran hukuncinsa.

A halin yanzu dai kotun ta tafi hutu na takaitaccen lokaci domin dawowa ta karanta hukuncinta kan karar da sauran bangarorin suka shigar kan zaben shugaban kasa na 2023.

Kotun fara ne da karanta hukucinta kan karar da jam’iyya APM ta shigar, kamar yadda alkalin, Haruna Tsauri ya sanar tun da farko.

Masu shigar da kara — jam’iyyun APM, PDP da LP  da ’yan takararsu — sun halarci zaman, haka ma bangaren wadanda ake kara, APC da shugaba Bola Tinubu.

Mataimakin Shugaban APC na Kasa, Abdullahi Ganduje ya halarci zaman tare da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da kuma gwamnoni hudu na jami’iyyar.

Sun zauna sa da shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP Iliya Damagun tare da mukarabbansa; da kuma shugaban LP, Emmanuel Abure — kowanne da lauyoyinsu.

Tun kafin fara zaman kotun aka tsaurara matakan tsaro a harabar kotun, wadda aka takaita halartar zaman ga mutanen da aka ba wa shaidar tantanceewa kadai.

A daura da kotun kuma, magoya baya sun yi cikar kwari, a yayin da kuma jami’an tsaro suka tsaurara matakai da kuma takaita zirga-zirga zuwa kotu.