A halin yanzu fitaccen malamin Musulunci da ke fuskantar shari’a kan zargin batanci ga Manzon Allah (SAW), Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, ya isa kotu inda za ta yanke masa hukunci.
Da misalin karfe 8.15 na safiyar Alhamis ne jami’an tsaro suka isa kotun Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu da ke garin Kano, inda aka ga malamin sanye da farin rawani da farar babbar riga da koriyar ’yar ciki.
- Waiwaye: Muhimman Abubuwa A Dambarwar Abduljabbar
- Na bai wa lauya N2m ya kai wa alkali don a sake ni —Abduljabbar
Aminiya ta lura cewa gabanin zaman kotun domin yanke hukuncin a ranar Alhamis, an tsaurara matakan tsaro a yankin Kofar Nasarawa da ke kusa da Fadar Sarkin Kano.
Dambarwar zargin malamin da batanci ga Manzon Allah (SAW) da aka shafe sama da shekara guda ana yi ta dauki hankali matuka, tun kafin batun ya kai ga gaban kotu a watan Yulin 2021.
Kotun za ta yanke hukuncin ne bayan shafe sama da wata 15 ana kai ruwa rana a gaban Mai Shari’ar Ibrahim Sarki Yola.
A halin yanzu manema labarai da masu rajin kare hakkin dan Adam na jiran fara zaman kotun domin yanke hukunci kan shari’ar da ta dade tana tayar da kura.