Sunan littattafai:
1-Rayuwar Mace: Daga Haihuwa Zuwa Tsufa
2-Soyayya Da Rayuwar Aure
3-Almajiranci Da Bara
Marubuciya: Mariya Inuwa Durumin Iya
Shekarar Wallafa: 2020
Kamfanin Wallafa: Gidan Dabino International, Kano
Mai Sharhi: Bashir Mudi Yakasai
Mafi yawan masu bincike da nazarce-nazarce kan harkokin rayuwar dan Adam a sha’anin rubuce-rubuce na adabi, adabin ma da ya jibinci rubutu na ilimi a fagen rayuwa ta bil Adama, a sha’nin zamantakewarsa da addininsa da siyasarsa da tattalin arzikinsa da kuma iliminsa na kimiyya da fasaha suna daukar wadannan mutane da ’yan baiwa; ba don komai ba sai don irin hikimar da suke da ita, wacce ta fi karfin duk wani mai tunani ba irin nasu ba.
Hajiya Mariya Inuwa Durumin Iya, dangane da shekaru ma iya cewa karama ce amma a hikima da basira, irin kwazon da take da shi, za mu kira ta babban kundin ilimi saboda irin gudunmawar da take bayarwa a wannan fage.
Marubuciyar ta yi bincike mai zurfi a rayuwar Malam Bahaushe ta yau, a sha’anin rayuwar mace daga haihuwa zuwa tsufa da soyayya da rayuwar aure a kasar Hausa da kuma almajiranci da bara.
Wadannan littattafai idan ka bi su daya bayan daya, za a ga tarin ilimi mai yawa a cikinsu. Misali, a littafin Rayuwar Mace Daga Haihuwa Zuwa Tsufa, ta bayani dalla-dalla a kan wace ce mace? Ta fito da mace filla-filla ta fuskar halitta da irin bambance-bambancenta da maza, ta fuskar daukar ciki da shayarwa da kwarewa ta fuskar rainon yara tun daga tushe. Idan tana yin bayani, kai ka ce likita ce. Idan ta sauya salo kai ka ce malamar addinin Musulunci ce saboda kawo hujjoji da ayoyin Alkur’ani Mai girma da Hadisan Manzon Allah (SAW). Wasu lokutan kai ka ce masaniyar zamantakewar al’umma ce.
Ta fito da matsaloli iri-iri da mace da ke wannan yanki na Najeriya ta Arewa, musamman Hausawa da Fulani da Kanuri da sauran kabilu da suke zaune tare. Yaya suke kallon mata a rayuwa bisa tasirin addini ko kum al’ada? Ta kuma fito da matsalolin da suke da alaka da zamani. Wani abin sha’awa da wannan littafi, shi ne yadda aka tsara shi daki-daki, wato matsala da maganinta daya bayan daya.
Magani daga iyaye, magani daga mahukunta, magani daga shugabannin addini, magani daga ’yan kasuwa, magani daga hukumomin da ba na gwamnati ba; uwa uba magani daga su mata tun suna kanana har zuwa tsufarsu, wato shirye-shirye na komawa ga Mahalicci.
Idan ka karanta wadannan littattafai na Mariya, za ka ga tsagwaron hikima ta rubutu da kuma nuni da tasirin fannonin ilimin addinin Musulunci da na zamani da ta samu a makarantun da ta halarta, kanana da manya.
Littafin Soyayya Da Rayuwar Aure A Kasar Hausa ya yi tsokaci sosai kan wannan batu. Mai karatu, mace ko namiji, babba da yaro za su fahimci cewa soyayya da aure zamantakewar rayuwa ce mai matukar muhimmanci a rayuwar al’umma, domin rashinsu ba karamar illa ba ce ga ma’aurata.
Mariya ta yi tambihi mai ratsa zukata a al’amuran soyayya da aure da kuma zamantakewa, inda ta yi nuni da cewa su ne turakun tallafar rayuwa, ta yadda idan kafa daya ta tasgade turakun murhun tukunyar da ke kan wuta, za ta zubar da abin da ke cikinta.
Da Mariya Inuwa ta dauki alkalaminta ta rubuta littafinta na uku na Almajiranci Da Bara, za ka cika da mamaki da kuma al’ajabi yadda ta sauya dungurungun da karanta mace a matsayinta mace da kuma karatuttukanta tun daga firamare da sakandare a makarantun mata zalla. Za ka ce babu mamaki idan har tana yin bayani game da mace. Amma abin sha’awar shi ne, da tana magana a kan almajiranci a Makarantar Allo na Tsangaya, sai ka daga mata farar tuta ta yabo.
Cikin hikima, Mariya ta yi bayanin yadda malamai suke samun almajiransu daga wajen iyayensu, tare da yadda suke zaben garuruwan da za su tafi, domin neman wannan karatu. Malaman sukan sauka ne a wajen hakimai ko dagatai ko masu unguwanni, ko kuma wadansu shahararrun malamai da suka fi su karatu, inda sau tari sarakuna suke neman malamai su shigo cikin kasarsu, domin koyar da mutanensu ilimi da koya musu sha’anin addini. A can baya, almajirai ba a sansu da barace-barace ba kamar yadda ake gani a yanzu. Suna samun abincinsu ne daga masaukin da suka sauka da makwabta da kuma ’yan aikace-aikace da suke yi na hidima a gidan Malam, kama daga noma da wanki da dibar ruwa da sauransu.
Daukacin littattafan marubuciyar, littattafai ne masu fadakarwa, ilimantarwa da yin nuni kan yadda za a shawo kan duk wata matsala da aka bijiro da ita, ga kuma nishadantarwa ta yadda ake sarrafa harshe. Horon da Mariya ta samu a sha’anin koyarwa, ya yi tasiri a rubutunta, musamman idan mutum ya kula da zubi da tsari na rubutun zai ga wannan a fili.
Wata basira da ta nuna a rubutunta, ita ce sanin al’adun Hausawa da Fulani da kuma Barebari na kawaici da kunya da rashin yin batsa a kasuwa.
Rubutunta babu Ingausa (wato cakuda Hausa da Ingilishi). Hausa take zubawa tsantsa kamar jakin Kano. Wani abin burgewa shi ne, idan Hajiya Mariya tana maganar rawar da gwamnati da kungiyoyi wadanda ba na gwamnati ba za su taka a sha’anin kananan yara, sai ka kira ta da ’yar gwagwarmayar kare hakkin dan Adam, domin tana amfani da lafuzza irin nasu.
Shawarata ga masu ruwa-da-tsaki da masu fada-a-ji da masu hannu-da-shuni su rika taimakawa wajen tallafa wa masu basira irin su Hajiya Mariya, ta yada ayyuka irin nasu ta fansar littattafanta da raba su a makarantu tun daga karamar sakandare har zuwa jami’o’i da manyan makarantun koyarwa da na fasaha da kimiyya da na sana’o’i da kuma share shiga jami’a. Bugu da kari littattafai irin nata, a rika karanta su a kafofin watsa labarai, musamman rediyo domin amfanin jama’a masu yawa. Ta haka ne kurum za a samu hanya mafi sauki wajen kawo sauyi a rayuwar al’ummarmu.
A karshe, ina fata masu ruwa-da-tsaki za su kalli wadannan ayyuka na Hajiya Mariya a matsayin mubudin kunne, wajen magance matsalolin da ta kawo cikin wadannan littattafai, musamman mace-macen aure a tsakanin Hausawa da barace-barace a Najeriya. Allah Ya kara mana mutane masu hali irin su Hajiya Mariya Inuwa Durumin Iya, domin samar da al’umma tagari, amin summa amin.